Yadda Aka Yiwa Wani Mai Gadin Kasuwa Yankan Rago A Wata Jahar Arewa, Yan Sanda Sun Kama Mutum 7
- Wasu miyagun mutane yiwa wani mai gadin kasuwa a Jos yankan rago a daren Asabar, 17 ga watan Satumba
- Yan sanda sun damke mutane bakwai da ake zargi a kan kisan mallam Muhammad Kabiru a kasuwan dare da ke garin Jos
- Marigayin ya shafe tsawon shekaru 15 yana gadi a kasuwan kuma yana daya daga cikin mutanen da aka aminta da su
Plateau - Rahotanni sun kawo cewa an tsinci gawar wani mai gadi, Muhammad Kabiru a Kasuwan Dare, wani sashi na babban kasuwan Jos a safiyar ranar Asabar.
Mahukuntan kasuwar sun ce an kashe marigayin wanda shine mai gadin kasuwan ta hanyar yi masa yankan rago da tsakar dare a lokacin da yake bakin aiki domin an tsinci gawar tasa ne a harabar kasuwan.
Da yake zantawa da jaridar Daily Trust kan lamarin, Shugaban Kasuwan Daren, Alhaji Jamilu Kabiru, ya ce:
“An tsinci mai gadinmu, daya daga cikin masu karfi kuma amintacce a kasuwan a mace an kashe shi.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
“Wani takwarana ne ya kirani a safiyar ranar Lahadi don ganin gawar. Babban abun bakin ciki ne wannan kuma mun yi rashi. Mun kai rahoton lamarin ofishin yan sanda.”
Ya ce mamacin ya shafe tsawon shekaru 15 yana aiki a matsayin mai gadi kuma basu taba samun matsala da shi ba.
Rundunar yan sanda ta yi martani
Daily Trust ta kuma rahoto cewa yayin da yake tabbatar da lamarin, kakakin rundunar yan sandan jihar Filato, DSP Alfred Alabo, ya ce an kama mutum bakwai da ake zargi yayin da ake bincike kan lamarin.
Alabo ya ce:
“DPO na yankin ya fara aiki kan lamarin. Saboda yanayi abun, an kama mutum bakwai da ake zargi. Ana kan gudanar da bincike. Muna kan lamarin.”
‘Yan Bindiga Sun Farmaki Coci, Sun Sace 40, Suna Neman Kudin Fansa N200m
A wani labari na daban, kungiyar mutanen kudancin Kaduna wato SOKAPU ta yi zargin cewa 'yan bindiga sun yi garkuwa da sama da mutum 40, harda yan coci a kwatas din Bayan Kasuwa da ke Kasuwan Magani, karamar hukumar Kajuru na jihar Kaduna.
A cikin wata sanarwa da shugaban kungiyar, Dr. Awemi Maisamari,ya gabatarwa manema labarai a Kaduna a ranar Litinin, ya ce yan bindigar sun tuntubi yan uwan wadanda aka sace inda suke nemi a biya naira miliyan 200 kafin su sake su.
A cewar kungiyar, lamarin ya afku ne a ranar 12 da 13 ga watan Satumba, a yankin Kasuwan Magani da ke karamar hukumar Kajuru, yan kilomita daga cikin birnin.
Asali: Legit.ng