Babbar Magana: Wani Matashi Ya Yi Barazanar Kashe Gwamnan APC

Babbar Magana: Wani Matashi Ya Yi Barazanar Kashe Gwamnan APC

  • Hukumar yan sandan Ebonyi ta gurfanar da wani matashi bayan ya yi barazanar kashe gwamnan jihar, David Umahi
  • Rundunar na kuma tuhumar mutumin mai suna Uche Awegbe da mallakar bindigogi da adduna
  • Ana kuma tuhumarsa da haddasa rikicin kabilanci tare da kashe wasu mazauna jihar biyu

Ebonyi - Rundunar yan sandan jihar Ebonyi ta gurfanar da wani mutum dan shekaru 40, Uche Awegbe, a gaban kotun Majistare na Abakaliki kan zargin barazanar kashe gwamnan jihar, David Umahi.

Yan sanda sun zargi Mista Awegbe da harbin mazauna jihar biyu har lahira da kuma haddasa rikicin kabilanci sau da dama a garin Effuim da ke karamar hukumar Ohaukwu, jaridar Leadership ta rahoto.

Rundunar tsaron ta kuma zargi mutumin da aika sakon barazanar kisa ga Gwamna Umahi ta wayar tarho.

Kara karanta wannan

Jerin Sunaye: Gwamna Ganduje Ya Ware biliyan N1.2 Don Ayyukan Hanyoyi 42

Umahi
Babbar Magana: Wani Matashi Ya Yi Barazanar Kashe Gwamnan APC Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Har ila yau, ana zargin mutumin wanda aka gurfanar a shari’a mai lamba MAB/634c/202, da mallakar bindigogi da adduna.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Dan sanda mai gabatar da kara, Sajan Obi Eberechukwu, ya zargi wanda ake kara da yiwa gwamnan barazana da ransa a ranar 19 ga watan Agustan 2022 a gida mai lamba 9, unguwar Umuoji, Abakaliki, babban birnin jihar ta hanyar tura sakon ta tarho.

Ya kuma zarge shi da mallakar bindigogi ba bisa ka’ida ba, tare da karfafa rikicin kabilanci a garin Effuim da ke karamar hukumar Ohaukwu na jihar a 2023, wanda yayi sanadiyar mutuwar wasu mazauna yankin.

Rahoton ya kuma kawo cewa kotun bata amsa rokom wanda ake kara ba saboda yanayin laifukan da ake zarginsa da aikatawa.

Mai shari’a a kotun, Linda Ogbodo, ta yi umurnin garkame Mista Awgbe a gidan gyara hali sannan ta dage shari’ar zuwa ranar 10 ga watan Oktoba.

Kara karanta wannan

Nasara Daga Allah: An Kama Wani Kasurgumin Ɗan Bindiga da Sojan Bogi a Jihar Zamfara

Ta umurci mai gabatar da kara da ya tura ainahin takardar shari’ar, shaidu da dukkanin takardun da ya shafi batun zuwa sashin DPP na jihar don jin shawararsu.

Aika-Aikar Dan China: Gwamnatina Za Ta Dauki Mataki Kan Makashin Ummita, Inji Ganduje

A wani na daban, gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano ta sha alwashin tabbatar da ganin doka ta yi aikinta a kan lamarin kisan Ummukhulthum Sani Buhari, da ake zargin wani dan kasar China da yi.

Da yake jawabi kan lamarin a gidan gwamnatin jihar, Ganduje ya ce dole maganar shari’a ta shigo ciki kuma sai doka ta yi aikinta tunda har abun ya danganci zubar da jini ne, sashin Hausa na BBC ta rahoto.

Gwamnan ya kuma bayyana cewa tuni suka sa aka tsare wanda ake zargin mai suna Mista Geng Quanrong, bayan jama’a sun kama shi a gidan iyayen marigayiyar a ranar Juma’ar da ta gabata.

Kara karanta wannan

Ana rikici a PDP, dan takarar shugaban kasa Atiku zai yi wata tafiya zuwa Turai

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng