'Yan Bindiga Sun Halaka Mutum Hudu, Sun Yi Garkuwa da Wasu 15 a Neja

'Yan Bindiga Sun Halaka Mutum Hudu, Sun Yi Garkuwa da Wasu 15 a Neja

  • 'Yan bindiga sun buɗe wa mutane wuta a ƙauyen Fapo dake yankin ƙaramar hukumar Lapai a jihar Neja, sun kashe mutane
  • Wani ganau ya shaida wa manema labarai cewa wannan ne karo na farko da irin haka ta faru a kauyen, maharan sun sace akalla mutum 15
  • Hukumar yan sanda reshen jihar Neja bata ce komai ba kan harin na baya-bayan nan duk da kiran da aka yi wa kakaki, DSP Wasiu Abiodun

Niger - Wasu miyagun yan bindiga sun kashe mutane huɗu, suka jikkata wasu Takwasa, sannan suka yi awon gaba da wasu mutum 15 a ƙauyen Fapo, ƙaramar hukumar Lapai a jihar Neja.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa lamarin wanda ya auku na ranar Lahadi, ya tarwatsa mazauna ƙauyen yayin da suka tsere neman mafaka lokacin da suka ji karar harbe-harbe.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Wani Bam Ya Fashe a Babban Birnin Jihar Arewacin Najeriya

Harin yan bindiga a jihar Neja.
'Yan Bindiga Sun Halaka Mutum Hudu, Sun Yi Garkuwa da Wasu 15 a Neja Hoto: punchng.com
Asali: Twitter

Wani ganau, Ɗanlami Idris, wanda ya zanta da manema labarai, yace 'yan ta'addan sun shiga kauyen da adadi mai yawa, suka buɗe wa mutane wuta kan mai uwa da wabi.

Idris yace maharan sun shafe awanni suna aikata ta'asa Kuma karo na farko kenan da yan bindiga suka kai makamancin harin ƙauyen.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Bamu taɓa ganin irin wannan harin ba kafin yanzu, harin ya yi muni sosai duba da rayukan da aka rasa da kuma yawan mutanen dake kwance suna jinya," inji Malam Idris.

Mutumin ya ƙara da yin kira ga gwamnati da hukumomin tsaro da su ƙara ƙaimi wajen sauke nauyin da Allah ya ɗora musu na kare rayuka da dukiyoyin al'umma domin dakile sake faruwar makamancin haka nan gaba a ƙauyen.

Yayin da aka nemi lambar kakakin hukumar yan sandan reshen jihar Neja, DSP Wasiu Abiodun, bai ɗaga kiran ba har zuwa yanzun da muke haɗa wannan rahoton.

Kara karanta wannan

Wasu Samari Sun Ba Hammata Iska Kan Budurwa Aisha a Nasarawa, An Illata Ɗaya

'Bam' Ya Fashe a Jalingo

A wani labarin kuma kun ji cewa Mutane Sun Shiga Tashin Hankali Yayin da 'Bam' Ya Fashe A Jalingo, jihar Taraba

Bayanai sun nuna cewa mutane sun shiga fargabar rashin sanin abinda zai faru nan gaba bayan aukuwar lamarin ranar Lahadi da daddare.

Wannan shi ne karo na huɗu da irin haka ta faru a birnin Jalingo bayan shigowar wannan shekarar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262