Kotu Ta Dauki Matakin Farko a Shari'ar Sojojin da Suka Kashe Sheikh Aisami a Yobe

Kotu Ta Dauki Matakin Farko a Shari'ar Sojojin da Suka Kashe Sheikh Aisami a Yobe

  • Babbar Kotu a Damaturu, babban birnin jihar Yobe ta ɗage zaman shari'ar korarrun Sojoji da suka kashe Sheikh Goni Aisami
  • Mai shari'a Amina Shehu ta ɗauki matakin ne bayan ɓangaren masu gabatar da ƙara sun nemi lokaci don tattara hujjoji
  • A watan Agusta da ya gabata ne, Wani Soja ya bindige Malamin bayan ya nemi ya rage masa hanya

Yobe - Babbar Kotu dake zama a Damaturu, babban birnin jihar Yobe ta ɗage zaman sauraron shari'ar korarrun Sojojin da ake zargi da kashe Sheikh Goni Aisami Gashuwa.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa Alƙalin dake jagorantar shari'ar, Mai Shari'a Amina Shehu, ta ɗage zaman zuwa ranar da ba'a sani ba bayan ɓangaren gwamnati sun nemi haka.

Yadda jami'an tsaro suka kai waɗanda ake zargi Kotu.
Kotu Ta Dauki Matakin Farko a Shari'ar Sojojin da Suka Kashe Sheikh Aisami a Yobe Hoto: thenation
Asali: UGC

Antoni Janar ma jihar Yobe, Barista Saleh Samanja, ya roƙi Kotun ta baiwa tawagarsa ta masu gabatar da ƙara isasshen lokaci domin su haɗa shaidu guri ɗaya don shari'ar ta tafi yadda ya kamata.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Jirgin Yaƙin Sojoji Ya Kai Sabon Harin Bama-Bamai Maɓoyar Bello Turji a Zamfara

Bayanai sun nuna cewa a ranar Litinin 19 ga watan Satumba, 2022 (yau) aka fara Ambatar Kes ɗin kisan a gaban Kotun.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Mai Shari'a Amina Shehu ta yanke cewa za'a sanar da kowane ɓangare da lamarin ya shafa sabuwar ranar da za'a ci gaba da shari'ar kan waɗanda ake zargi.

Legit.ng Hausa ta tattaro cewa tawagar jami'an yan sanda sun kawo mutum biyu da ake zargi Kotun yau Litinin.

Waiwaiye kan yadda lamarin ya faru

A watan Agusta da ya gabata, Wani Soja da ya nemi Marigayi Sheikh Aisami ya rage masa hanya, ya yi ajalinsa da nufin sace motarsa a Gashuwa.

Yan sanda sun kama Sojoji biyu da suka taras a wurin bayan sanar musu da abinda ke faruwa. Da suka tsananta bincike Sojan ya labarta duk abinda ya faru.

Bayan binciken da hukumar sojin Najeriya ta gudanar kan lamarin, ta sanar da korar sojojin biyu daga bakin aiki tare da damƙa su hannun hukumar yan sanda domin su gurbi ɗanyen aikin da suka shuka.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Wani Bam Ya Fashe a Babban Birnin Jihar Arewacin Najeriya

A wani labarin kuma Kotu Ta Yanke Hukunci Kan Karar Da PDP Ta Shigar Na Neman Haramtawa Tinubu Da Obi Yin Takara

Babban kotun tarayya da ke zamanta a Abuja ta yi watsi da karar da jam'iyyar PDP ta shigar na neman a soke takarar Bola Tinubu na jam'iyyar APC da Peter Obi na Labour Party.

A karar mai lamba FHC/ABJ/CS/1016/2022, PDP ta kallubalanci sauya yan yan takarar mataimakan shugaban kasa da APC da Labour Party suka yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262