EFCC Ta Gurfanar da Surukin Obasanjo, Tsohon Ma’aikacin Banki a Gaban Kuliya

EFCC Ta Gurfanar da Surukin Obasanjo, Tsohon Ma’aikacin Banki a Gaban Kuliya

  • Hukumar EFCC ta kai karar wasu mutum biyu kotu a Legas, tana zarginsu da amfani da kayan da ba nasu ba
  • Daya daga ciki, an tattaro cewa, kani ne ga marigayiyi matar tsohon shugaban kasan Najeriya, Obasanjo
  • Sai dai, lokacin da ake tambayar gaskiyar lamari, sun dage cewa basu aikata laifin ba, kuma sun nemi beli

Legas - EFCC ta gurfanar da Dr John Abebe, kanin marigayiyi matar tsohon shugaban kasa Obasanjo, Stella a gaban kotun laifuffuka na musamman a ranar Litinin a Ikeja ta jihar Legas.

Rahoton da muke samu ya bayyana cewa, EFCC na zargin Dr Abebe ne da aikata dabi'ar nan ta zamba, Punch ta ruwaito.

An maka surukin tsohon shugaban kasa Obasanjo a kotu
EFCC Ta Gurfanar da Surukin Obasanjo, Tsohon Ma’aikacin Banki a Gaban Kuliya | Hoto: punchng.com
Source: UGC

An gurfanar da sirikin na tsohon shugaban kasa ne tare da tsohon shugaban wani banki, Kamoru Alade Oladimeji a gaban mai shari'a Olubunmi Abike-Fadipe a kan tuhume-tuhume shida da suka hada da hada baki, sata, da kuma karkatar kudi.

Kara karanta wannan

Babbar Magana: Wani Matashi Ya Yi Barazanar Kashe Gwamnan APC

Mai shari'a ya karanto musu laifukansu da cewa, ko sun amince sun yi babakeren kadarar da ta tai N120m mallakin Arsenal Technologies Limited?

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakazalika, an tuhume su da hada baki wajen karya da karbar kudade a lokuta daban-daban tare da ikrarin mallakar wasu gine-gine a Legas.

A cewar EFCC, laifukan da ake tuhumarsu akai sun saba sashe na 280(1), (12), 8 (7), 285(1) da 278(1)(b) na kudin manyan laifuka na jihar Legas, 2011.

Martanin wadanda ake tuhuma

Bayan sauraran batun mai shari'a, wadanda ake tuhumar sun musanta zargin da ake musu, inda suka dage basu aikata ba, Tori ta tattaro.

Bayan da suka musanta zargin, mai gabatar da kara, Sulaimon ya nemi kotu da ta sanya ranar shari’a tare da tsare mutanen biyu a hannun hukumar kula da hali ta Najeriya har sai an yanke hukunci.

Sai dai, lauyoyin wadanda ake tuhuma, Anthony Popo daSam Etaifo ya bukaci kotu ta bashi belin wadanda yake kare duba da 'yancin da suke dashi.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Wata cuta ta kama kama Nnamdi Kanu a hannun DSS, inji lauyansa

Bayan sauraran batutuwa, mai shari'a ta ba da belin surukin bisa tarar N20m tare da kawo mutum daya mai tsaya masa.

Hakazalika, an ba da beli mutum na biyun da ake hukuma akan N10m da kuma mutum daya da zai tsaya masa, mazaunin jihar Legas.

An Datsi Tashar Yanar Gizon INEC Daga Asiya a Lokutan Zaben Gwamnan Jihar Ekiti da Osun

A wani labarin, akwai yiwuwar a samu matsala a babban zaben 2023 yayin da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta sanar da sabon tsaiko a shafinta na duba sakamakon zaben (IReV).

Wani tahoton TheCable ya ce, INEC ta bude sirri, tace wasu madatsa daga nahiyar Asiya sun datsi tashar duba sakamakon zabe a zabukan da suka kammala na jihohin Ekiti da Osun.

Shugaban INEC, Mahmud Yakubu ne ya bayyana wannan lamari a yau Juma'a 9 ga watan Satumba a Abuja yayin da yake magana a wani taron da ya shafi jami'an sakamakon zabe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and leads the Hausa Desk at Legit.ng. He is AfricaCheck's ambassador and HumAngle Technology and Civic Impact Fellow. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. His commitment to excellence has earned him recognition, including the Legit Fearless Team Player of the Year 2023 and 2024 Distinguished Editorial Leadership Award. Email: salisu.ibrahim@corp.legit.ng