Bidiyon Macen Farko 'Yar Najeriya da ta Siyawa Kanta Iphone 14 Pro Max da Guminta Ya Janyo Cece-kuce
- Wata budurwa ‘yar Najeriya da bata siya IPhone 12 ko 13 ba lokacin da ta fito ta siya iPhone 14 Pro Max
- Kwana daya kafin ta siya wayar, an sanar mata cewa guda daya tak na kirar wayar za a kawo garinta don haka ta hanzarta zuwa siya
- ‘Yan Najeriyan da suka kalla bidiyon sun taya ta murna yayin da wasu suka dinga mata ba’a kan cewa ita ce mace ta farko da ta siya da guminta
Wata budurwa ‘yar Najeriya ta bar jama’a baki bude bayan ta wallafa bidiyon kanta da IPhone 14 Pro Max da ta siya da kudinta.
A bidiyon da ta fitar, ta bayyana yadda ta je shagon siyar da waya domin siyawa kanta. Daya daga cikin ma’aikatan shagon ya bukaci ta bude wayar don ya gani.
Mamallakiyar Iphone 14 cike da farin ciki
Budurwar 'yar Najeriya tace duk da ta siya wayar da kudinta da ta adana, tana matukar farin ciki da mallakarta.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Sai da ta bukaci masu shagon wayar da su ajiye mata saboda guda daya tilo suka kawo.
Daga latsa fuskar wayar har sau biyu, a take wayar ta bayyana mata "Hello".
Kalla bidiyon a kasa:
Jama'a sun yi martani
Zuwa lokacin rubuta wannan rahoton, wallafar ta samu sama da tsokaci 1,000 yayin da mutum sama da 600,000 suka kalla bidiyon.
Legit.ng ta tattaro muku wasu daga cikin stokacin jama'a.
oshonubidayo yace:
"Ina taya ki murna,Afrika ta baki lambar yabon zama mace ta farko da ta siya sabuwar wayar da kudinta."
promzy559@ tace:
"Na taya ki murna, ni bani da ma Iphone 6."
kantinkayawskinny tace:
"Budurwa ta farko da ta fara siyan Iphone da kudinta, ina taya ki murna."
zainabami125 Zain tace:
"Zan siya tawa kila idan 18 ta fito, a yanzu dai bari in cigaba da manejin iPhone X di ta."
emini_Mullar yace:
"Wayyo Allah, wa zai taimaka min?"
Bidiyon Babur Mai Tashi Sama na Farko da aka Kera a Duniya, Za a Siyar da shi Sama da N300m
A wani labari na daban, Reuters ta rahoto cewa, XTURISMO shi ne babur na farko a duniya mai tashi sama yayin da aka gwada aikinsa a Amurka.
Kamar yadda rahoto daga kafar yada labaran ta bayyana, babur din zai iya lulawa sararin samaniya ya kwashe mintuna 40 yayin da yake zura gudu a kan mita 62 duk sa'a daya.
Asali: Legit.ng