Daliban Sun Fito Zanga-Zanga, Sun Tare Hanyar Filin Jirgin Saman Legas Saboda Yajin Aikin ASUU
- Wani bidiyo ya nuna lokacin da matasa suka mamaye wani titin jihar Legas domin nuna dawa da yajin aikin ASUU
- Matasan suna ta rera wakokin neman gwamnati ta waiwayi ASUU, kana ASUU din ma ta duba bukatar dalibai
- Daliban jami'a a Najeriya na kama sana'a tun bayan da yajin aikin ASUU ya kara kamari, ya kuma fara jan watanni
Jihar Legas - Wani bidiyon da jaridar Tribune Online ta yada ya nuna lokacin da matasa dalibai suka yi dandazo tare da toshe titin tashar jirgin saman jihar Legas.
Bidiyon ya nuna tarin matasa suna wake-waken nuna adawa da ci gaba da yajin aikin kungiyar malaman jami'o'in Najeriya (ASUU).
Idan baku manta ba, ASUU ta shiga yajin aiki tun watan Fabrairun bana, kuma har yanzu tana ci gaba da yajin saboda gwamnati ta gaza cika mata alkawarorin da ta dauka.
A koke-koken da matasa ke yi, sun sha daura alhakin ci gaba da yajin aikin ga malamansu da suka ki janyewa, yayin da malaman ke ci gaba kallon laifin gwamnati.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Sun toshe hanyar filin jirgin saman Murtala Mohammed dake Legas
A sabon bidiyon da muka gani a yau Litinin 19 ga watan Satumba, matasan sun yi dafifi wajen nuna kokensu.
An ga wasu daga cikinsu sanye da riguna masu dauke da rubutun rokon a kawo karshen yajin aiki, wasu kuwa na tikar rawa a kan titi.
Hakazalika, akwai 'yan sanda da kuma wasu daliban da ke daukar hotuna tare da yadawa a kafafen sada zumunta.
Kalli bidiyon:
'Yan Sanda Sun Fatattaki 'Yan a Mutun Peter Obi da Suka Fara Gangami a Jihar Ebonyi
A wani labarin, rundunar 'yan sandan jihar Ebonyi ta fatattaki dandazon jama'ar da suka taru a Abakaliki a dandazon mutum miliyan magoya bayan dan takarar shugaban kasan LP, Peter Obi.
Rahoton The Nation ya ce, masoya Obi sun taru ne a Pastoral Centre dake Abakaliki, inda 'yan sanda suka fatattake su da barkonon tsohuwa.
An ce lamarin ya haifar da cunkoson ababen hawa a titin Old Enugu a birnin na Abakaliki a yau Asabar 17 ga watan Satumba.
Asali: Legit.ng