Sojojin Sama Sun Yi Luguden Wuta A Sansanin Gogarman Yan Bindiga Bello Turji
- Dakarun sojojin saman Najeriya sun yi luguden wuta kan sansanin rikakken ‘dan bindiga Bello Turji
- Kamar yadda majiya ta bayyana, jiragen yakin sun saki makamai masu linzami yankin Fakai inda gidan Turji yake
- A halin yanzu ba a san yawan ‘yan ta’addan da suka rasa rayukansu ba amma an tabbatar da shekawar da yawa lahira
Zamfara - Yan bindiga masu tarin yawa na sansanin fitaccen ‘dan ta’adda Bello Turji, sun sheka lahira, jaridar PR Nigeria ta rahoto.
An halaka ‘yan ta’addan ne a wani samamen ba-zata da dakarun sojin rundunar Operation Forest Sanity suka kai dazukan Zamfara.
Harin ba-zatan an yi shi ne da jiragen yakin sojin sama bayan sun samu bayanan sirri.
Wata majiyar sirri ta sanar da PRNigeria cewa jiragen NAF din sun harba makamai masu linzami yankin Fakai, inda aka gano shi ne gidan Turji, a matsayin wani bangare na yaki da ta’addanci a yankin Shinkafi.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Majiya ta ce:
“A halin yanzu, ba zamu iya bayyana yawan wadanda aka halaka ba.”
'Ni Na Rika Yi Wa Yan Bindiga Magani,' Fasinjar Jirgin Kaduna Da Ya Samu Yanci Ya Magantu
A wani rahoton, Mustapha Imam, daya daga cikin mutanen da yan bindiga suka sace jirgin kasar Kaduna zuwa Abuja ya ce ya yi wa yan bindiga magani a lokacin da ya ke tsare a hannunsu.
A wani bidiyon da Tukur Mamu, mawallafin Desert Herald wanda ya taimaka wurin tattaunawa don ganin an sake su, fasinjan ya bayyana zamansa a hannun yan bindigan a matsayin 'lamari matukar muni'.
Imam, wanda ma'aikaci ne a jami'ar Usman Danfodiyo da ke Sokoto, ya ce ba zai yi wa makiyinsa fatan shiga halin da ya tsinci kansa ba.
Asali: Legit.ng