Bidiyo: Hirar Karshe Da Budurwar Da Dan China Ya Kashe Tayi Da Kawarta, Ya Kasance Akan Mutuwa

Bidiyo: Hirar Karshe Da Budurwar Da Dan China Ya Kashe Tayi Da Kawarta, Ya Kasance Akan Mutuwa

  • Wani mutun 'dan kasar China ya halaka budurwa a unguwar Janbulo da ke jihar Kano ta hanyar caka mata wuka
  • Bidiyon Marigayiya Ummita da kawarta sarauniya ya bayyana a shafukan soshiyal midiya inda suke hira kan mutuwa
  • Wannan hirar tasu ta taba zukatan jama'a da dama musamman yadda marigayiyar ta nuna tawali'u a zantukarta, tana mai cewa kowa da tasa kaddarar

Kano - A yau ne Al’ummar unguwar Janbulo dake karamar hukumar Kumbotso ta jihar Kano suka wayi gari da wani mummunan al’amari na kisan wata matashiya mai suna Ummita.

Wani mutumin kasar China ne ya bi budurwar mai shekaru 23 har cikin dakinta da ke gidan iyayenta sannan ya yanka ta da wuka.

A daidai lokacin da jama’a ke jimamin wannan al’amari sai ga wani bidiyo na hirar da marigayiyar tayi da wata kawarta mai suna Sarauniya.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: 'Dan China Ya Sokawa Budurwarsa Mai Shekaru 23 Wuka a Kano, Ta Sheka Lahira

Marigayiya
Bidiyo: Hirar Karshe Da Budurwar Da Dan China Ya Kashe Tayi Da Kawarta, Ya Kasance Akan Mutuwa Hoto: PM News
Asali: UGC

A cikin bidiyon wanda shafin diaryofanorthernwoman ya wallafa a Instagram, an gano suna hira da sarauniya kuma hirar tasu ta karkata ne a kan mutuwa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kawar tata tace tana burin ta riga marigayiya Ummita mutuwa inda ita kuma tace sam tana iya fara mutuwa domin kowa da kaddararta.

Harma tayi misali cewa tana iya kwanciya yanzu nan sai Allah ya amshi ranta domin Shi Ubangiji babu ruwansa.

Sarauniya tace:

“Ummita yanzu idan na mutu wannan bidiyo din za ki dunga tunawa dani ko? Na mutu, Allah yasa mu cika da kyau da imani, Allah yasa muyi kyakkyawar karshe.

Sai marigayiyar ta amsa da:

“ Sarauniya ina ga ma in rigaki mutuwa. Sarauniya baki san Allah ba kaddarar kowa zuwa take yi, yau zan iya kwanciya in fadi in mutu. Toh Allah yasa mu cika da kyau da imani kuma ma bazaki rigani mutuwa ba har sai kin haifi ‘ya’ya.”

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari Za ta Kirkiro Bankuna na Musamman Domin Matasan Najeriya

Wannan bidiyo ya taba zukatan mutane da dama inda suka yi mata fatan samun Rahamar Ubangiji.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

itx_shama56 ta yi martani:

"Innalillahi wainna illairrajiun, Subhanallah Allah ya mata Rahama Ameen."

babyncee ta ce:

"Innalillahi wainna ilhair rajiun."

_halal_space ya rubuta:

"Ameen ya rabbi. This shud b d video trending not d other one. Allah ka sa ta huta shi kuma Allah ya bada ikon hukunta shi w/out biase. Allah ya sa namu idan tazo tayi kyau."

meram_thani ta ce:

"Ya Salam!!! Allah yasa aljannar ce makomarta da mu baki daya. This is so sad."

asmeer_exclusive_fabrics ta ce:

"Tabbas babu waazin da yafi mutuwa kana tare da mutum yau gobe babu shiAllah ya gafarta miki."

'Dan China Ya Sokawa Budurwarsa Mai Shekaru 23 Wuka a Kano, Ta Sheka Lahira

Mun kawo a baya cewa wani mutun 'dan kasar China ya sokawa budurwarsa mai shekaru 23 wuka inda ta mutu a take a kwatas din Janbulo dake karamar hukumar Kumbotso ta jihar Kano.

Kara karanta wannan

Dan Najeriya ya jawo cece-kuce yayin da ya fara birgima a kasa lokacin da matarsa ta haihu

Lamarin ya faru ne wurin karfe 10 na daren Juma'a bayan wanda ake zargin ya kai wa budurwa mai suna UmmaKulsum Sani Buhari ziyara a gidan iyayenta dake kusa da ofishin National Environmental Standards and Regulations Enforcement Agency (NESREA).

Yayin da abinda ya hada masoyan biyu har yanzu ba a gano shi ba, Daily Trust ta tattaro cewa likitoci sun tabbatar da mutuwar budurwar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng