Bulabuduwaye, Shugaban Masu Zartarwa na Boko Haram da Iyalansa ya Tuba, Ya Mika Wuya Wurin Soji
- Bashir Bulabuduwaye, babban kwamanda kuma shugaban masu zartar da hukuncin kisa na Boko Haram ya tuba tare da iyalansa
- Bulabuduwaye ya halaka sojoji da farar hula sama da 1,000 don ya sha bayyana bidiyoyin 'yan ta'addan yana kaddamar da hukucin kisa tare da kiran jama'a kafirai
- An gano cewa, ya tuba ne sakamakon rashin abinci da ambaliyar ruwa da ta addabi maboyarsa da kuma tsoron 'yan ISWAP dake nemansa ido rufe
Borno - Shugaba masu zartarwa na Boko Haram, Bashir Bulabuduwaye, wanda ke da alhakin yanka dukkan wadanda aka yi garkuwa da su a karkashin umarnin kungiyar, ya mika kansa hannun rundunar sojin Najeriya.
Ya mika wuya tare da iyalansa da suka hada da matansa da 'ya'yansa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An tattaro cewa, 'dan ta'addan da iyalansa sun mika wuya hannun dakarun Operation Hadin Kai dake Banki a karamar hukumar Bama ta jihar Borno a ranar 12 ga watan Satumban 2022.
Wani jami'in sirri ya sanar da Zagazola Makama, kwararre a fannin yaki da ta'addanci a yankin tafkin Chadi, cewa Bulabuduwaye sanannen 'dan ta'adda ne dake kaddamar da hukuncin kisa ga jama'a, sojojin da aka kama ko farar hula tun lokacin da Abubakar Shekau yake shugabancinsu.
Majiyoyin sun ce tsohon 'dan ta'addan ya bayyana a bidiyoyi daban-daban da mayakan Jamā'at Ahl as-Sunnah lid-Da'wah wa'l-Jihād suka bayyana yana tsinke makogwaron wadanda suka kama da kuma harbe jama'a bayan an zargesu da zama kafirai.
Majiyoyin sun bayyana cewa, Bulabuduwaye da tawagar masu kaddamarwa sun halaka a kalla mutum 1,000 da aka kama tare da yankewa hukuncin kisa.
Yace Bulabuduwaye yana daga cikin kwamandojin da suka tsere a shekarar da ta gabata bayan tsagin ISWAP sun kai musu harin ba-zata a watan Mayun 2021 wanda hakan ya janyo sanadin mutuwar Abubakar Shekau.
"Ya bar su yayin da ya ki yin mubaya'a ga ISIS inda ya kafa sansani a kauyen Kote dake Banki inda yake boye tare da sauran mayakan."
"Ya mika wuya ne sakamakon rugugin wutar da dakarun sojin sama ke yi da kuma wanda sojin kasa na Opertaion Hadin Kai ke biyo baya da shi."
- Majiya ta sanar.
Ya gagara samun abinci da sauran abubuwan bukata ga kuma ambaliyar ruwa wacce ta addabi maboyarsu. Yana kuma tsoron yaki da ISWAP kasantuwarsa daya daga cikin wadanda aka bukaci a halaka saboda ya ki mubaya, wata majiya ta tabbatar.
Bayan Kwanaki 186 da Sace Fasinjojin Jirgin Kasa, Mutum 23 Suka Rage Hannun 'Yan Ta'adda
A wani labari na daban, ashirin da uku daga cikin fasinjojin harin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna suna hannun 'yan ta'adda bayan kwanaki 186 da sace su.
Daily Trust ta rahoto cewa, sama da fasinjoji 60 ne aka sace a farmakin jirgin kasa daga Abuja zuwa Kaduna.
Asali: Legit.ng