Kama Tukur Mamu Ba Zai Hana Tattaunawar Sako Fasinjojin Jirgin Kasan Abuja-Kaduna Ba, Gwamnatin Buhari
- Gwamnatin tarayya ta ce tana da masu tattaunawa da 'yan ta'adda domin tabbatar da sako fasinjojin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna
- Hukumar DSS ta kame daya daga cikin masu shiga tsakani, Alhaji Tukur Mamu bisa zarginsa da shiga harkar ta'addanci
- An sace matafiya a watan Maris din da ya gabata, lamarin da ya girgiza 'yan Najeriya da dama a ciki da wajen kasa
FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya ta yi tsokaci cewa, kama mawallafin jaridar Desert Heral, Alhaji Tukur Mamu ba zai kawo tsauko ga tattaunawar sakin fasinjojin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna ba.
Mamu, wanda hadimi ne ga Sheikh Gumi ya kasance mai shiga tsakanin 'yan bindiga da iyalan jama'ar da aka sace a harin jirgin Abuja-Kaduna a watan Maris din bana, Punch ta ruwaito.
Ci gaba: Najeriya ta samu karuwa, Buhari ya ba Turawa da 'yan wasu kasashe shaidar zama 'yan Najeriya
Da yake zantawa da manema labarai bayan tattaunawar tsaro da ya yi shugaba Buhari, ministan harkokin 'yan sanda Muhammadu Dingyadi ya ce akwai wasu mutane daban dake tattauna sakin fasinjojin.
Jaridar TheCable ta rahoto Dingyadi na cewa:
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
"Ana ta kokarin ceto dukkan 'yan Najeriyan da ke kodai hannun masu garkuwa da mutane ko 'yan bindiga, kuma ba za mu bar komai da zai kai ga sakinsu ba.
"DSS ta kame Mamu saboda wata dabi'ar da ta saba manufa da gudanarwa da kula da tsaro game da mutanen da aka sace da kuke magana a kai.
"Lamarin yanzu yana kotu, kuma kotu ta yi abinda ya dace. Ba za mu bar wata kafa da zata kai ga sakin 'yan uwanmu maza da mata ba da har yanzu suke tsare.
"Watakila kunsan Mamu ne saboda ya bayyana kansa karara. Akwai wadanda suke shiga tsakani dake magana a madadin wadanda aka sace.
"Akwai iyaye; akwai jami'an tsaro; duk muna tattaunawa. Saboda haka, kada kuce don an kama Mamu batun tattaunawa da shiga tsakani ta kare.
Yadda aka kama Mamu
Idan baku manta ba, mun kawo muku rahoton yadda aka kama Tukur Mamu a kasar Masar a daidai lokacin da yake kan hanyarsa ta zuwa kasar Saudiyya.
Kwanaki bayan kame shi, DSS ta shaidawa kotu cewa, Mamu zai tafi Saudiyya ne domin ganawa da wasu shugabannin 'yan ta'adda na kasa da kasa.
Daga nan ne kotu ta ba hukumar ta tsaro ci gaba da titsiye mawallafin har na tsawon kwanaki 60 don zakulo gaskiya.
A tun farko, 'yan ta'adda sun kai hari tashan jirgin kasa da ke kan hanyar Abuja zuwa Kaduna, Channels Television ta ruwaito.
Majiyoyi sun ce yan ta'adda sun saka bam ne a kan layin dogon hakan ya tilasta wa jirgin da ya baro Abuja zuwa Kaduna ya dakata, Nigerian Tribune ta rahoto.
Wannan shine hari na biyu da yan ta'addan ke kai wa a hanyar ta Kaduna zuwa Abuja.
Asali: Legit.ng