Gwamnatin Buhari Za ta Kirkiro Bankuna na Musamman Domin Matasan Najeriya
- Ministan harkokin wasanni da matasa na kasar nan yace ana shirin rikidar da tsarin nan na NYIF
- Sunday Dare ya shaidawa Duniya cewa ana so gidauniyar ta zama banki ta yadda za a tallafawa matasa
- Dare ya bayyana irin kokarin da gwamnatin tarayya take yi domin ganin matasa sun cin ma burinsu
Abuja - Ministan wasanni da matasa a Najeriya, Sunday Dare ya bayyana cewa gwamnati na kokarin maida tsarin gidauniyar NYIF ya zama banki.
Daily Trust ta rahoto Sunday Dare yana mai wannan jawabi a ranar Alhamis bayan wani taro da aka yi a fadar shugaban kasa da ke birnin tarayya Abuja.
Dare yake cewa da zarar majalisar zartarwa ta FEC ta amince da wannan yunkuri, za a samar da bankuna na musamman da zai kula da matasan kasar nan.
Ministan cigaban matasa da wasannin yake cewa idan an kafa wannan banki, zai maida hankali wajen samar da bashi da jari ga matasan ‘yan kasuwa.
A cewar Mai girma Ministan, manufar irin wannan banki ita ce bunkasa kasuwancin masu matsakaicin shekaru domin taimakawa rayuwarsu.
Kamar yadda Vanguard ta fitar da wannan labari jiya, daukacin N75bn da shugaba Muhammadu Buhari ya warewa NYF za su tafi ne wajen koyon sana’a.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Idan aka samu wanda yake da kwarewa da sana’a, za a ba shi kudin da zai taimaka masa.
Gidauniyar NYIF za ta koma banki
Karshen tikawa shi ne gidauniyar tallafin gwamnatin tarayya ta zama banki na cigaban matasa. A tarihi, ba a taba samun irin wannan bankin ba.
A jawabin da ya yi wa manema labari a Aso Villa, Ministan yace tuni matasa fiye da 31, 000 sun amfana da gidauniyar da gwamnatin Buhari ta kawo.
An amincewa matasa 45, 000 su karbi bashi daga NYIF, amma zuwa yanzu mutum 31, 000 aka samu sun karbi wadannan kudi daga N250, 000 zuwa N3m.
A bangaren horar da mutane, an rahoto Dare yace ma’aikatarsa ta hada-kai da kamfanin Halogen wajen horar da matasa 61, 000 kan tsaron yanar gizo.
Matatun mai za su tashi
An ji labari Gwamnatin Muhammadu Buhari tana kokarin ganin ana tace gangunan danyen mai a Najeriya a maimakon a dogara da kasashen waje.
Timipre Sylva yace zuwa Disamba za a karasa gyara tsohuwar matatar Fatakwal, sannan ana kokarin ganin matatun Kaduna da Warri sun tashi.
Asali: Legit.ng