'Yan Bindiga Sun Hallaka Dan Banga, Sun Sace Mutane da Yawa a Neja

'Yan Bindiga Sun Hallaka Dan Banga, Sun Sace Mutane da Yawa a Neja

  • Rahoton da muke samu daga majiya ya shaida cewa, wasu 'yan ta'adda sun kai farmaki wani yankin jihar Neja
  • An hallaka dan banga daya, yayin da aka jikkata wani a harin da aka kai cikin ofishin 'yan banga a yankin
  • Jihohin Arewa maso Yammacin Najeriya na yawan fuskantar hare-hare, mazauna na koka halin da ake ciki

Lapai, jihar Neja - 'Yan bindiga a jihar Neja sun kashe wani dan banga sun kuma raunata wani da harbin bindiga a yankin Ebbo ya karamar hukumar Lapai a jihar Neja.

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa, an kuma yi awon gaba da wasu 'yan kauye da dama a yankin na jihar Neja.

An ruwaito cewa, 'yan ta'addan sun farmaki Ebbo ne da misalin karfe 10:45 na dare, inda suka tafi kai tsaye ga ofishin 'yan bangan.

Kara karanta wannan

Hotuna: Dakarun Soji Sun Kai Harin Kwantan Bauna, Sun Halaka 'Yan Boko Haram 7 a Borno

'Yan bindiga sun hallaka dan banga a Neja
'Yan Bindiga Sun Hallaka Dan Banga, Sun Sace Mutane da Yawa a Neja | Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Harin na zuwa ne kwanaki hudu bayan da aka farmaki yankunan Kpada da Yaba, wasu yankuna dake makwabtaka da babban birnin tarayya Abuja, inda aka kashe mutum daya tare da tarwatsa mazauna.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yadda harin ya auku a yankunan Neja

Mazauna yankin sun ce tsagerun sun kuma farmaki Angwan Dajin Gomna a yankin Kpada inda suka yi garkuwa da mutane biyar kafin su wuce kauyen Zago da kuma Lafiyan Zago inda suka dauki sa'o'i suna barna.

A yankin Zago kadai, an ce sun yi awon gaba da mutane sama da 10, rahoton Vanguard.

Mazauna yankunan sun shaidawa Daily Trust cewa, ana yawan samun hare-haren 'yan ta'adda a 'yan watannin nan, lamarin da ke kara sanya tsoro a zukatan mazauna.

Malam Yusuf Adalami, wanda shine shugaban 'yan bangan ya shaida cewa, an tattara dan bangan da ya jikkata zuwa babban asibitin Gulu yayin da sauran jami'an 'yan bangan ke bin diddigin inda 'yan ta'addan suka shiga.

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da 'yan bindiga suka tsare uwa da jaririnta, suna neman fansan miliyoyi

Ba a samu jin ta bakin mai magana da yawun 'yan sandan jihar Neja, DSP Wasiu Abiodun har zuwa lokacin hada wannan rahoton saboda wayarsa bata shiga.

'Yan Sanda Sun Ceto Wata Uwa da Danta da Tsageru Suka Sace a Jihar Kwara

A wani labarin, rahoton Premium Times ya ce, ‘yan sanda a jihar Kwara sun ceto wata mata da danta da aka sace bayan wani dauki ba dadi tsageru a wani aikin ceto da ‘yan sanda, 'yan banga da mafarauta suka yi.

Jami’in hulda da jama’a na ‘yan sandamn jiharr, Okasanmi Ajayi ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba a Ilorin.

A cewar sanarwar: "A ranar 13 ga Satumba, da misalin karfe 11:20 na dare, an sace Afusat Lawal da danta, Taofeek Lawal, aka tafi da su."

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.