Bidiyon Yadda Fasto Ya Jawo Cece-Kuce Yayin da Ya Daura Auren Wani Mutum da Mata Uku Nan Take

Bidiyon Yadda Fasto Ya Jawo Cece-Kuce Yayin da Ya Daura Auren Wani Mutum da Mata Uku Nan Take

  • Wani kirista ya ba da mamaki yayin da ya auri mata har uku a rana guda a cocin da ake kira Primitive Church
  • Mutumin mai suna Byamunggu Kanjira Prosper ya bayyana cikin farin ciki lokacin da aka ga hotunansa da amarensa guda uku
  • A hakan, fasto ne ya daura musu igiyar aure cikin alfahari, kuma da yawan wadanda aka gani a bidiyon basu dauki hakan komai ba

Kongo - Wani cocin addinin kirista da ake kira Primitive Church ya daura auren wani mutum da amarensa har guda uku a nan take.

Sabanin wasu cocin addinin kirista, wannan coci dai na goyon bayan auren mace fiye da daya, kuma ya ba mambobinsa damar auren adadin matan da suke so.

Yadda fasto ya aurar da mata uku ga wani mamban cocinsa
Jama'a na ta cece-kuce yayin da wani ya auri mata uku a coci | Hoto: YouTube/Afrimax English
Asali: UGC

Ba matsala bane a auri mace fiye da daya a cocin

Kara karanta wannan

A Raba Aurenmu Don Baya Aikin Komai Sai Jajibe-jajiben Fada, Matar Aure Ta Roki Kotu

A wani faifan bidiyon da Afrimax English ya fitar a YouTube, an ga faston cocin na daura auren Byamungu Kanjira Prosper tare da matansa uku da ya kawo domin ya aure su.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bidiyon ya bayyana cewa, cocin yana can ne a Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo a nahiyar Afrika.

Shi dai wannan ango ya ce, bai zama dole mutum ya kame ya tsaya da auren mace daya kacal ba.

A cewarsa, ganin adadin matan da ake dasu a duniya, lokaci na zuwa nan kusa da mata 7 za su auri mutum daya.

Don haka ya shawarci mata, ya ce su zo cocin nan nasu domin samun miji cikin sauki ba kama r yadda saura coci suke ba a duniya.

Kalli bidiyon:

Martanin jama'a

Mutane da dama sun bayyana kadan daga yadda suka ji da ganin wannan bidiyo na Prosper.

Kara karanta wannan

Ruwan dare: Budurwa ta jawo cece-kuce yayin da ta kammala digiri, tace za ta rushe gidansu

Heather ya ce:

"Al'ummar Tsohon Alkawari sun yi irin wadannan abubuwan a karkashin doka, auren mace fiye da daya tabbas ya faru amma fa karewa ya yi cikin rudani."

Lino Gomic yayi sharhi:

"Wannan labarin kadai ya sake sanya Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango ta zama wata kasar yawon bude ido mai dumi, abin burgewa ne."

Susie yeye

"Ba karamin abin bakin ciki bane ganin yadda wannan faston ya yaudari jama'a da sauran kasashen duniya. Mutane na biye mashi don kawai su yi aure ba kan gado.. Allah ka yafe masu domin basu san me suke ba."

An Kama Malamar Coci da Yara 15, Ta Ce N50,000 Take Sayen Yaro Daya

A wani labarin, wata malamar coci mai suna Maureen Wechinwu dake fataucin yara kanana ta shiga hannun jami’an rundunar ‘yan sandan jihar Ribas.

Rahoton jaridar Vanguard ya ce, rundunar ta kuma gurfanar da wasu mutum 20 da aka kama tsakanin watan Agusta zuwa Satumba bisa laifuka daban-daban.

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da 'yan bindiga suka tsare uwa da jaririnta, suna neman fansan miliyoyi

Bayan samun bayanan sirri, 'yan sanda sun kama Maureen a gidanta dake Aluu ta karamar hukumar Ikwerre a jihar Ribas, tare da ceto yara kanana har 15 daga gidanta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.