Bincike Ya Nuna Sai Talakan Najeriya Ya Shekara 3 Yana Asusu Kafin Ya Iya Sayen Sabuwar iPhone 14 Pro

Bincike Ya Nuna Sai Talakan Najeriya Ya Shekara 3 Yana Asusu Kafin Ya Iya Sayen Sabuwar iPhone 14 Pro

  • Rahotanni sun ce, kamfanin Apple ya yi bikin sanar da fitowar sabbin wayoyin IPhone 14 a kasar Amurka
  • To amma ya tsadar wayar take ga 'yan Najeriya? Bincike ya bayyana adadin kudin da ake siyar da wayoyin
  • Wayoyin IPhone wasu nau'ikan wayoyi ne da 'yan Najeriya ke yiwa kallon 'ga talaka sai dai kallo'

Kamfanin Apple ya sanar da fito da jerangiyar sabbin wayoyin IPhone 14 dke da wasu abubuwa masu ban mamaki.

Duk da cewa farashinsu ka iya zama daidai da yadda aka saki wayoyin kamfanin a baya, a wannan karon zai ba dan Najeriya wahala ya iya saye.

Wannan kuwa ya faru ne sakamakon karyewar farashin Naira, lamarin da zai iya sa farashin wayoyin ya zama mai tudu da yawa.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: 'Yan Arewa sun fi karbar Tinubu fiye da Atiku da Kwankwaso, inji jigon APC

Adadin kudin da ake siyar da iPhone 14 a Najeriya
Bincike ya nuna sai talakan Najeriya ya shekara 3 yana asusu kafin ya iya sayen sabuwar IPhone 14 Pro | Hoto: Tuite/AFP
Asali: Getty Images

Ga matsaikacin dan Najeriya, zai iya shafe shekaru uku yana zunzurutun aiki kafin iya tara kudin da zai sayi sabuwar IPhone.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar shafin yanar gizon Apple, farashin iPhone 14 Pro (254GB) zai kai kusan ko sama da $1099.

Me hakan ke nufi ga 'yan Najeriya?

Idan aka sauya $1099 zuwa Naira ta Najeriya, akalla kudin wayar zai kai N479,713, nan ma idan aka sauya $1 a matsayin N436.50; farashin dala mafi rahusa.

Ganin yadda wahalar samun dala ke kara muni, akwai yiwuwar dillalan iPhone su yi kudinta da farashin dala a kasuwar 'yan canji ba wai gwamnati ba.

Ya zuwa ranar 13 ga watan Satumba, farashin dala ya kai akalla N705, wanda hakan zai kara kudin iPhone ya zama kusan N774,795.

Wakilin Legit.ng Hausa ya tambayi wani dillalin canji kudi a jihar Gombe, Muhammadu Sa'ad kan nawa ne farashin dala.

Kara karanta wannan

Al-Mustapha Ya Fashe Da Kuka Ya Zubar Da Hawaye Kan Rashin Tsaro A Najeriya

Yace a yau Talata, 13 ga watan Satumba ya sayi dala a kan N702, sannan ya siyar N707.

Karshe ma wani rahoto ya nuna cewa, farashin iPhone 14 Pro a Najeriya zai iya kai NGN1,440,000 a jihar Legas da kuma NGN1,540,000 a wajen jihar ta Legas (6GB RAM + 256GB ROM.)

Kwanaki nawa mutum zai shafe kafin iya sayen iPhone?

Gurguwar shawara ce ga dan Najeriyan dake da albashin N30,000 ya yi tunanin sayen sabuwar iPhone 14.

Hasashe ya nuna cewa, akalla irin wannan ma'aikaci zai shafe shekaru uku dinda yana tikar aiki kafin ya iya tara kudin iPhone.

Wannan fa kenan, inda a cikin N30,000 dinnan ba a taba ko anini ba, kawai asusu za a yi na tsawon lokacin.

Kalli jerin albashi da asusun siyan iPhone 14

AlbashiAsusun siyan iPhone 14
N30,000Watanni 37
N50,000Watanni 23
N100,000Watanni 12
N150,000Watanni 9

Budurwa Ta Kammala Digiri, Ya Sha Alwashin Rushe Gidansu Na Kasa Sannan Ta Gyara Shi

Kara karanta wannan

Yadda Asibiti Suka Rike Gawar Yarinya Saboda Iyayenta Sun Kasa Biyan N400,000 na Magani

A wani labarin, wata matashiyar da ta kammala karatunta na digiri ta ba da mamaki a kafar sada zumunta yayin da dauki hoto a gaban wata bukka da tace gidansu ne.

Sai dai, budurwar bata zo da wasa ba, domin kuwa ta sha alwashin sauya wannan gidan bukka ya zama katafaren gida, lamarin da ya girgiza jama'a.

Mujallar Squad ce ta yada wannan hoton a wani sakon da ta wallafa a shafinta na Facebook.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.