A Raba Aurenmu Don Baya Aikin Komai Sai Jajibe-jajiben Fada, Matar Aure Ta Roki Kotu

A Raba Aurenmu Don Baya Aikin Komai Sai Jajibe-jajiben Fada, Matar Aure Ta Roki Kotu

  • Matar aure mai suna Florence Ideye ta roki kotu da ta raba aurensu da mijinta Victor saboda baya fita nema kuma yana yawan zuke-zuken hayaki
  • Victor ya ce yana daukar dawainiyar iyalinsa don kaninsa na aike masa kudi sosai, ya ce har shaguna guda biyar ya budewa matar tasa da sana'o'i iri-iri
  • Mijin ya ce abun da ya fahimta da matar tasa, soyayyar kudi take yi domin yanzu kanin nasa ya daina aike masu da kudi

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Lagos - Wata yar kasuwa da ke neman a raba auransu da mijinta, Florence Ideye, a ranar Talata, ta fada ma kotun Igando da ke jihar Lagas cewa maigidanta Victor, ya ki aiki tsawon shekaru 10 da suka gabata.

Misis Ideye ta kuma yi zargin cewa mijin nata na son shaye-shaye da yawan fadace-fadace, jaridar Premium Times ta rahoto.

Kara karanta wannan

Akwai Aiki A gaba: Sanatan PDP Ya Bayyana Abun Da Zai Faru Idan Ayu Ya Yi Murabus

Matar wacce ke zaune a yankin Ijegun, jihar Lagas, ta kara da cewa babu sauran soyayya a tsakaninsu.

Sandar kotu
A Raba Aurenmu Don Baya Aikin Komai Sai Jajibe-jajiben Fada, Matar Aure Ta Roki Kotu Hoto: Thisdaylive
Asali: UGC

Ta bayyana cewa mijin nata ya dogara ne a kan kaninsa, wanda ya kasance don kwallon kafa, don kula da iyalinsa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mista Ideye yaya ne ga tsohon dan wasan Super Eagles, Brown Ideye.

Ta ce:

“Abun bakin ciki, kanin nasa ya yanke mu, ya ce ba zai iya jure takuran ba.
“Shi (Victor) ya ce yana son tafiya waje, saboda haka ya siyar da kayayyakinsa a matsayinsa na makaniki. Har zuwa yau, yana sa ran zai yi tafiya kuma ya ki aiki.
“Zai tura yaranmu su siyo masa karan sigari da barasan leda. Tura yaran siyo irin wadannan abubuwan yasa sam raina bai kwanta ba.
“Na gaji, tuni na koma gidan ubana.”

Mijin nata ya yi bayanin abun da ke faruwa

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da 'yan bindiga suka tsare uwa da jaririnta, suna neman fansan miliyoyi

Da yake martani, Mista Ideye ya ce ya yi aiki a matsayin direba a wata makarantar firamare tsawon shekaru hudu kuma ana biyansa N15,000 duk wata.

Ya ce akwai kyakkyawar alaka tsakaninsa da yaransa, yana mai cewa ya kashe kudaden da dan uwansa ya aike masa kan iyalinsa.

Ya ce:

“An taba yi mata fashi kuma tsawon watanni shida bata yi aiki ba. Nine nake yin komai, kanina ma ya aike mata N650,000 don taimakawa, amma duk da haka tana korafi.
“Na bude mata kusan shaguna biyar sannan na gina ta kan kasuwanci daban-daban. Komai ya tsaya ne lokacin da dan uwana ya daina turo da kudi.
“Na san abun da take kokarin fadi shine: idan babu kudi, babu soyayya."

Shugaban kotun, Adeniyi Koledoye, ya dage zaman zuwa 11 ga watan Oktoba don yanke hukunci, The Eagle ta rahoto.

Matashi Ya Sharbi Kuka Da Hawaye Bayan Ya Gano Cewa An Yi Baikon Budurwarsa Da Wani

Kara karanta wannan

Alkali Ya Tura Dan Sufetan Yan Sanda Gidan Yari Kan Satar Motar N52m A Legas

A wani labarin kuma, mun ji cewa wani dan Najeriya ya fashe da kuka mai tsuma rai bayan ya gano cewa an rigada an yi baikon budurwarsa da wani.

Matashin a cikin wani sakon murya da ke yawo a shafukan soshiyal midiya, ya ba da labarin mawuyacin halin da ya shiga yayin da yake bayyana cewa baida masaniya game da cin amanarsa da take yi.

Wani bidiyo ya nuno shi yana kuka wiwi bayan wani ya kwace masa budurwar tasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng