Saurayi da Budurwa Sun Sayar Da Jaririn da Suka Haifa Kafin Fatiha Kan N500,000

Saurayi da Budurwa Sun Sayar Da Jaririn da Suka Haifa Kafin Fatiha Kan N500,000

  • Dakarun 'yan sanda sun kama wata matashiyar budurwa da Saurayinta kan sayar da jaririnsu na kafin aure a Ebonyi
  • Kakakin hukumar 'yan sandan jihar, SP Chris Anyanwu, yace masoyan sun haifi ɗan babu aure suka sayar da shi N500,000
  • Bayan haka 'yan sanda sun cafke wasu hatsabiban ɓarayin kananan yara da suka shahara a sata da garkuwa

Ebonyi - Hukumar 'yan sanda a jihar Ebonyi ta kama wata matashiya yar shekara 20, mahaifiyar wani jariri namiji da kuma masoyinta, waɗan suka sayar da ɗansu ga wata mai gidan Reno kan kudi N500,000.

Mahaifiyar mai suna, Ola China, daga ƙauyen Amangwu Edda, ƙaramar hukumar Afikpo ta arewa a jihar Ebonyi, saurayinta ya ɗirka mata ciki ne a watan Agusta, 2021.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Wani Abu Ya Fashe da Mutane, Ya Yi Mummunar Ɓarna a Jihar Jigawa

Hukumar yan sanda.
Saurayi da Budurwa Sun Sayar Da Jaririn da Suka Haifa Kafin Fatiha Kan N500,000 Hoto: vanguard
Asali: UGC

Vanguard ta ruwaito cewa Ola ta haihu ne a watan Afrilu, 2022 a Obigbo, jihar Ribas, inda ta koma gidan gwaggonta domin rainon cikin.

Bayan Allah ya sauke ta lafiya, Ola ta haɗa baki da Saurayinta Uban jaririn mai suna, Jonah Ogbuagu, suka sayar da jaririn.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kakakin hukumar 'yan sandan Ebonyi, SP Chris Anyanwu, a ranar Talata, yace sun kama mai gidan Renon jarirai wacce tafi shahara da Mama Abigail a garin Ovima, ƙaramar hukumar Afikpo ta arewa.

A wata sanarwa a Abakaliki, kakakin 'yan sandan yace:

"Mama Abigail tana tafiyar da gidan renon yara wanda take amfani da shi domin lulluɓe haramtaccen kasuwancinta. Tuni aka damƙa waɗanda ake zargin hannun hukumar hana safarar mutane ta ƙasa domin ɗaukar mataki na gaba."

Yan sanda sun kama ɓarayin yara

Ya ƙara da cewa yan sanda sun kama tawagar mutum biyu masu safarar ƙananan yara, waɗan da suka yi ƙaurin suna wajen sace wa, garkuwa da kuma cefanar da yara.

Kara karanta wannan

Adamawa: An biyashi N5000 da kwanon Shinkafa 4 don yayi kisan kai, ya kashe mutum 1, ya bar daya na jinya

Anyanwu ya ba da bayansu da Otuu Chizaram, 24, daga Ndukwe Akpoha da kuma Agbi Precious, 20, daga Evuma Road duk a ƙaramar hukumar Afikpo ta arewa a jihar Ebonyi, kamar yadɗa Daily Trust ta ruwaito.

A wani labarin kuma Matashi Ya Sharbi Kuka Da Hawaye Bayan Ya Gano Cewa An Yi Baikon Budurwarsa Da Wani

Wani dan Najeriya ya fashe da kuka mai tsuma rai bayan ya gano cewa an rigada an yi baikon budurwarsa da wani.

Matashin a cikin wani sakon murya da ke yawo a shafukan soshiyal midiya, ya ba da labarin mawuyacin halin da ya shiga yayin da yake bayyana cewa baida masaniya game da cin amanarsa da take yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262