Adamawa: An Biyashi N5000 Da Kwanon Shinkafa 4 Don Yayi Kisan Kai, Ya Aikata

Adamawa: An Biyashi N5000 Da Kwanon Shinkafa 4 Don Yayi Kisan Kai, Ya Aikata

  • Mutumin Adamawa ya sa bankawa Ango da Amarya wuta saboda amaryar ta yaudaresa bayan sun yi alkawarin aure
  • Wanda aka baiwa aikin kisan ya aikata hakan bayan biyansa Naira Dubu Biyar da kwanon shinkafa 4
  • Amaryar ta mutu a asibiti sakamakon gobarar yayinda shi kuma Ango yana asibiti rai hannun Ubangiji

Hukumar yan sandan jihar Adamawa na neman wanda aka baiwa kwangilan kashe Amarya da Ango ruwa a jallo.

Mutumin mai suna Ibrahim Savanna ya aikata aika-aikan ne bayan biyansa kudi N5000 da kwanon shinkafa hudu.

Bayan karban kudin da shinkafar, Ibrahim Savanna, ya bankawa gidan amarya wuta cikin dare.

Wani mutumin jihar Adamawa, Ibrahim Muhammadu, ne ya bashi aikin bankawa Amarya da Ango wuta saboda matar ya yaudaresa.

Kara karanta wannan

Ta Yaudareshi Bayan Kashe Mata N150,000 Ta Auri Wani: Mutumin Yola Ya Bankawa Amarya Da Ango Wuta

An tattaro cewa Ibrahim magidanci ne mai yara hudu amma ya fada rumbun soyayya da Amaryar har ya kashe mata kudi N150,000 bayan sun yi alkawarin aure

Ibrahim ya baiwa Savanna aikin banka wuta ranar 6 ga watan Satumba, 2022.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan abu ya faru makonni biyu kacal bayan auren Amaryar da Ango.

TheNation ta ruwaito cewa daga baya Amaryar ta mutu a asibiti sakamakon raunukan da ta samu a gobarar yayinda shi kuma Ango yana asibiti rai hannun Ubangiji.

Adamawa
Adamawa: An Biyashi N5000 Da Kwanon Shinkafa 4 Don Yayi Kisan Kai, Ya Aikata
Asali: UGC

Har yanzu ana neman Ibrahim Savannah Ruwa a Jallo

Kakakin hukumar yan sandan jihar, SP Suleman Nguroje, ya tabbatar da aukuwan lamarin inda yace an kaddamar da bincike kuma za'a gurfanar da shi a kotu.

Ya bada tabbacin cewa lallai za'a hukunta mutumin kuma kada mutane su dau doka a hannu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel