2019: Yadda Obasanjo ya gudanar da zanga - zanga a jihar Ogun

2019: Yadda Obasanjo ya gudanar da zanga - zanga a jihar Ogun

- An gudanar da zanga - zanga jihar Ogun

- Tsohon shugaban kasa Obasanjo ne ya jagoranci zanga - zangar

- Ya ambaci rashin ko in kula da gwamnati take yi, akan abinda yake kawo tashe - tashen hankali

Tsohon shugaban kasa Olusegun obasanjo ya kaddamar da wata kungiya ta wucin gadi don ci gaban Nageriya a jihar Ogun.

2019: Obasanjo ya gudanar da zanga - zanga a jihar Ogun
2019: Obasanjo ya gudanar da zanga - zanga a jihar Ogun

Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya kaddamar da wata kungiya ta wucin gadi don Ci gaban nageriya ba da jimawa ba a jihar ogun.

Tsohon shugaban kasar, wanda ya ziyarci Iwe Ironhin NUJ press center, oke Ilewo, Abeokuta, Tare da Donald Duke da Olagunsoye Oyinlola Tsofaffain gwamnonin jihar Cross Rivers da Osun, Gboyeya Nasiru Isiaka, Mrs. Modupe Adelaja da babban dan siyasan nan daga jam'iyar APC da PDP.

Obasanjo ya bayyana cewar wasikar sa ga Buhari satin da ta gabata baiyi ta domin cin mutunci ba face damuwar sa da son samun mafita ga kasar baki daya.

Ya kara da cewar Najeriya a matsayin ta ta kasa baza ta cigaba da kasuwanci ba yadda ya kamata, duba da cewa tun lokacin da aka samu yan cin kai ba a samu cigaba ba, akwai bukatar a tsaya a yi tunanin ma fita don cigaban kasa.

2019: Obasanjo ya gudanar da zanga - zanga a jihar Ogun
2019: Obasanjo ya gudanar da zanga - zanga a jihar Ogun

Obasanjo wanda ya ce Najeriya a matsayin ko wace kasa, tana da kalubale iri iri, ya kara da cewa ba kaddamar da wannan kungiya ne don ta wayar wa yan Najeriya kai wajen samun zaman lafiya, hadin kai, tsaro da kaunar juna mai dorewa musamman mata da matasa don kawo karshen fada ce fadace a kasa.

ya kara da cewa samar da wannan kungiya ta samo asali sakamakon kashe kashe da akeyi , karya dokoki , rashin biyayya ga kundin doka ta tarayya tare da durkushewar tattalin arziki a karkashin jagorancin gwamnatin shugaba Buhari

Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo, ya kaddamar da zanga - zanga a jihar Ogun. Tsohon shugaban kasar, wanda isa wurin taron tare da magoya bayan sa da suka yi mashi rakiya, irin su tsohon gwamnan jihar Cross River, Donald Duke, da tsohon gwamnan jihar Osun, Olagunsoye Oyinlola, Gboyega Nasiru Isiaka, Misis Modupe AAdelaja da sauran manyan 'yan siyasa daga jam'iyun APC da PDP.

A lokacin da yake jawabi a taron, tsohon shugaban kasar yace wasikar da yayi zuwa ga shugaba Buhari a makon daya gabata yayi tane ba bisa ka'ida ba, duk da dai cewar jimamin yanda kasar take ciki ne yasa shi rubuta wasikar. Ya kara da cewar, bai kamata Najeriya mu cigaba da zama cikin duhun rayuwa ba.

DUBA WANNAN: Gwamnatin tarayya tana shirin dakatar da kwastam daga shiga kasuwanni

"Idan har hanyar da aka bi tun lokacin neman 'yancin kai bata yi mana amfani ba, kamata yayi mu nemi wata hanyar daban wacce zata yi mana amfani."

Tsohon shugaban kasar ya jaddada cewar, Najeriya, tana fuskantar matsaloli da dama, ya bayyana cewar sun gudanar da zanga - zangar ne domin kawo, hadin kan al'umma, zaman lafiya, tsaro da kwanciyar hankali, musamman ma akan matasa.

Ya ambaci rashin ko in kula da gwamnatin tarayya take yi a matsayin abubuwan da suke kawo tashe - tashen hankali a kasar nan, da kuma yanayin da tattalin arzikin kasar nan ya shiga a kar kashin mulkin shugaba Buhari shine dalilin yin zanga - zangar.

Idan ba a manta ba satin daya gabata Legit.ng ta kawo muku rahoton wasikar da tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo yayi wa shugaba Buhari, wacce ta dinga kawo cece kuce a tsakanin al'ummar kasar nan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng