Dan Sarki A Najeriya Ya Gayyaci 'Ƴan Kungiyar Asiri' Su Kashe Mahaifinsa Saboda Wata Sabani
- Yan sanda a Jihar Ogun sun yi nasarar kama wasu matasa shida da ake zargi da yunkurin kashe wani basarake a Illaro, Jihar Ogun
- Matasan da ake zargin yan kungiyar asiri ne sun bayyana cewa dan basaraken ne ya gayyace su su taho su kashe mahaifinsa
- Kwamishinan yan sandan Ogun, Lanre Bankole, ya umurci a tura wadanda ake zargi sashin bincike na SCID daga bisani a gurfanar da su a kotu
Ogun - Dan wani mai sarautar gargajiya a garin Oja-Odan na Illaro a Jihar Ogun ya gayyaci wasu da ake zargin yan kungiyar asiri ne su kashe mahaifinsa kan rikicin da ke tsakaninsu da mahaifiyarsa.
Rundunar yan sandan a ranar Litinin ta tabbatar da kama mutum shidan da ake zargi yan kungiyar asiri wadanda aka ce sun yi yunkurin kashe basaraken.
Hatsabibin Dan Bindiga Boderi Ya Tsallake Rijiya Da Baya A Yayin Da Sojoji Suka Kashe Mataimakinsa Da Wasu
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Kakakin yan sanda a jihar, SP Abimbola Oyeyemi, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa a Ota, Jihar Ogun, Daily Trust ta rahoto.
Sunayen wadanda aka kama a fadar basaraken na Ogun - Oyeyemi
Oyeyemi ya bada sunan wadanda ake zargin kamar haka; Michael Ayodele, Monday Samuel, Ademola Matthew, Hammed Jelili, Ogundele Ojeh da Sunkanmi Fadina.
Kakakin yan sandan ya ce:
"An kama su ne bayan kiran neman dauki da aka samu a hedkwatar Oja odan daga Oba na kasar Gbokoto, Oba G.O Olukunle, misalin karfe 4.25 na yamma cewa wasu yan kungiyar asiri sun zo za su kashe shi a fadarsa.
"Bayan samun kiran, DPO na Oja-Odan, cikin gaggawa ya tattara jami'ansa suka isa fadar suka tarar bata garin na harbe-harbe.
"Yan sandan suka yi musayar wuta da su kuma suka ci galaba kansu har suka kama shida cikinsu.
"Yayin musu tambayoyi, wadanda ake zargin sun ce su mambobin kungiyar asiri ta Eiye ne."
Ya cigaba da cewa:
"Sun kuma sanar da yan sandan cewa dan basaraken wanda ya yanzu ake nemansa, ne ya gayyace su don su halaka shi saboda wani matsala da ke tsakaninsa da mahaifiyarsa."
Kwamishinan yan sandan Ogun ya umurci zurfafa bincike kan wadanda ake zargin
Kakakin yan sandan ya ce an kwato bindiga kirar gida (Double Barrell) harsashi da wasu makaman da wurin wadanda ake zargin.
Ya kara da cewa, dan basaraken da yanzu ake nema, ya tsere da wani bindigan mallakar yan kungiyar.
Kwamishinan yan sanda, Lanre Bankole ya bada umurnin a tura wadanda ake zargin sashin binciken manyan laifuka da nufin gurfanar da su a kotu da zarar an kammala bincike.
Kwamishinan ya kuma ce an fara bincike don gano dan sarkin da ya tsere, don shima ya girbi abin da ya shuka.
Yadda Fasto Ya Saka Ni Na Kashe Mahaifiya Ta Da Adda, Mata Mai Shekara 30
A wani rahoton, rundunar yan sanda na jihar Ondo ta kama wata mata, Blessing Jimoh, mai shekaru 30 saboda kashe mahiyarta, Ijeoma Odo The Nation ta ruwaito.
Blessing ta ce ta halaka mahaifiyarta da adda bayan fasto ya fada mata cewa mahaifiyar mayya ce.
An yi holen ta tare da wasu da ake zargi da aikata laifuka daban-daban.
Asali: Legit.ng