Gwamnatin Buhari Ta Shawarci ’Yan Najeriya Su Gaggauta Goge Wasu Manhajojin Na’ura
- NCC ta shawarci ‘yan Najeriyan dake amfani da wasu manhajojin 'Google Chrome Extension' guda biyar da su gaggauta goge su
- Hukumar ta NCC ta yi gargadin cewa, an kirkiri wadannan manhajoji ne domin su saci bayanan jama'a haka siddan
- Abin ban mamakin ma shi ne, manhajojin da NCC ta lissafa ba sabbi bane, domin kuwa sama mutane miliyan daya ne suka daukesu a na'urorinsu
Hukumar Kula da Harkokin Sadarwar ta Najeriya ta gano wasu abubuwan da ka iya kawo tsaiko ga 'ya kasa a kan manhajar Google Chrome.
A cewar hukumar, irin wadannan manhajoji na bin diddigin duk wasu shafuka da mai amfani dasu ke bi.
NCC ta bayyana hakan ne a wata sanarwa da ta wallafa a shafin yanar gizo, wanda Legit.ng ta gani.
Manhajojin guda biyar da NCC tace 'yan su gujewa
- McAfee Mobile
- Netflix Party/Netflix Party 2
- Full Page Screenshot Capture Screenshotting
- FlipShope Price Tracker Extension
- AutoBuy Flash Sales
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
NCC ta yi gargadin cewa, duk da akwai mutum sama da miliyan 1.4 dake amfani da manhajojin, duk da haka akwai hadarori da ke tattare dasu idan ba a kula ba.
Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa, NCC ta ce akwai manhajojhi da yawa da Google suka cire a ma'ajiyar manhajoji Web Store, to amma abu ne mai wahala iya tsaftace kafar ta yanar gizo.
A bangare guda, NCC ta shawarci masu amfani da wayoyin hannu da sauran abubuwan zamani da su ke karatun ta natsu kafin sauke manhaja a na'ur'rinsu.
Ana amfani da Chrome Extensions a na'urorin teburi da na tafi d agidanta, kana ana amfani da irin manhajojin da NCC ke gargadi a kai a wayoyin hannu.
An Datsi Tashar Yanar Gizon INEC Daga Asiya a Lokutan Zaben Gwamnan Jihar Ekiti da Osun
A wani labarin, akwai yiwuwar a samu matsala a babban zaben 2023 yayin da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta sanar da sabon tsaiko a shafinta na duba sakamakon zaben (IReV).
Wani tahoton TheCable ya ce, INEC ta bude sirri, tace wasu madatsa daga nahiyar Asiya sun datsi tashar duba sakamakon zabe a zabukan da suka kammala na jihohin Ekiti da Osun.
Shugaban INEC, Mahmud Yakubu ne ya bayyana wannan lamari a yau Juma'a 9 ga watan Satumba a Abuja yayin da yake magana a wani taron da ya shafi jami'an sakamakon zabe.
Asali: Legit.ng