Da Duminsa: Sanata Ubah Ya Magantu Kan Yunkurin Halaka shi da 'Yan Bindiga Suka yi
- Sanata Ifeanyi Ubah ya tabbatar da farmakin da 'yan bindiga suka kai masa tare da tawagarsa a jihar Anambra
- Sanatan ya sanar da cewa, an halaka wasu daga cikin 'yan sanda da jami'an DSS dake tare da shi a tawagar
- Kwamishinan 'yan sandan jihar, Echeng Echeng ya ziyarci inda lamarin ya faru kuma ya ga yadda lamarin ya kazanta
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Awka, Anambra - A ranar Litinin, Sanata Ifeanyi Ubah ya tabbatar da mutuwar wasu daga cikin hadimansa da masu tsaron lafiyarsa a yayin farmakin da aka kai wa tawagarsa a ranar Lahadi.
An kai wa tawagar Sanatan farmaki a wurin kasuwar Nkwo Enugwu dake karamar hukumar Njikoka ta jihar Anambra, jaridar P.M News ta rahoto.
Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya rahoto cewa, 'yan bindigan sun budewa tawagar wuta inda suka bar wasu matattu har da mutum biyu da ba a cikin tawagar suke ba.
Tashin Hankali: An Shiga Zullumi Bayan An Gano Gawar Dalibai Mata 3 Na Jami'ar Najeriya A Dakin Kwanansu
Sanatan wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai a ranar Litinin a Awka, yace makasan sun halaka wani Obum Ikechukwu da Goodness Mathias.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ubah ya kara da cewa, wasu daga cikin masu tsaron lafiyarsa daga hukumar 'yan sanda da hukumar tsaron sirri duk an halaka su.
DSP Toochukwu Ikenga, kakakin rundunar 'yan sandan jihar Anambra, ya tabbatar da aukuwar lamarin amma bai bayar da bayani kan yawan wadanda lamarin ya ritsa da su ba.
"Kwamishinan 'yan sanda, Echeng Echeng ya ziyarci inda lamarin ya faru kuma an samu jini a wurin dake tabbatar da lamarin ba mai sauki bane, amma ba zan iya bayyana yawan wadanda suka rasa rayukansu ba."
- Yace.
Yan Bindiga Sun Budewa Sanata Ubah Wuta, An Kashe Akalla Mutum 6
A wani labari na daban, 'yan Bindiga sun budewa tawagar motocin Sanata Ifeanyi Ubah wuta a garin Enugwu-Ukwu dake karamar hukumar Njikoka dake jihar Anambra ranar Lahadi.
Bidiyon da aka dauka bayan harin ya nuna cewa ana hasashen kimanin yan sandan shida aka kashe a musayar wutar, rahoton SaharaReporters.
Wata majiya a riwayar Punch ta bayyana cewa:
"Wasu bata gari sun kaiwa Sanata Ifenyi Ubah hari a Enugwu Ukwu. Wannan shiryayyen hari ne. Kwantan bauna sukayi masa."
Asali: Legit.ng