An Shiga Zullumi Bayan An Gano Gawar Dalibai Mata 3 Na Jami'ar Najeriya A Dakin Kwanansu

An Shiga Zullumi Bayan An Gano Gawar Dalibai Mata 3 Na Jami'ar Najeriya A Dakin Kwanansu

  • An shiga zullumi da damuwa bayan gano gawarwakin wasu dalibai mata uku a dakin kwanansu na jami'ar COOU a jihar Anambra
  • Dakta Harrison Madubueze, mai magana da yawun jami'ar ya tabbatar da lamarin yana mai cewa jami'an tsaro su fara bincike
  • Madubueze ya ce hukumar makarantar ba su san daliban suna makaranta ba domin an yi hutu tun ranar 24 ga watan Agustan 2022

Anambra - An tsinci gawar dalibai mata na jami'ar Chukwuemeka Odumegwu Ojukwu, (COOU), na Igbariam, Jihar Anambra a ranar Asabar a dakin kwanansu, The Punch ta rahoto.

Wata majiya ta bayyana sunan daliban kamar haka; Obidiaso Chidera ( Aji 2, Kimiyyar Siyasa), Mercy (Aji 2, Kimiyyar Hada Magunguna), da Emmanuella (200-level Business Administration).

Taswirar Jihar Anambra
An Tsinci Gawar Dalibai Mata 3 A Dakin Kwanansu Na Jami'ar Anambra. Hoto: @MobilePunch.
Asali: UGC

A halin yanzu ba a san abin da ya yi sanadin mutuwarsu ba, amma ana zargin sun rufe kansu ne a cikin dakin bisa kuskure.

Kara karanta wannan

An Bayar da Belin Mawakin Najeriya Ice Prince, Kotu ta Saka Ranar Cigaba da Shari'a

Amma, hukumar makarantar ta ce jami'an tsaro na bincike kan lamarin kuma za a sanar da abin da suka gano a lokacin da ya dace.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Abin da majiya ta ce game da mutuwar daliban jami'ar Anambra

Majiyar ta ce:

"Daliban suna rufe a cikin dakinsu. Da muka bude dakin, mun ga gawar biyu cikinsu a kan gadajensu, yayin da ta ukunsu muka gano gawarta a dakin girki."

Yayin da ta ke tabbatar da lamarin, hukumar makarantar ta ce mutuwar daliban ya girgiza ta.

Mai magana da yawun jami'ar Dr Harrison Madubueze ya ce makarantar ta girgiza bayan samun labarin.

Ya ce:

"Jami'an tsaro suna bincike kan lamarin, za su sanar da abin da suka gano a lokacin da ya dace."

Madubueze ya ce jami'ar ba ta san cewa daliban na aji biyu zuwa sama har yanzu suna zaune a harabar jami'ar ba.

Kara karanta wannan

2023: Atiku ya gana da wasu tsoffin shugabannin siyasar kasar nan, sun yi wata tattaunawa

Ya cigaba da cewa:

"An rufe makaranta a ranar Laraba 24 ga watan Agustan 2022 bayan kammala jarrabawar zango na biyu kuma za a dawo karatu ranar 1 ga watan Oktoban 2022."

El-Rufai zai sake yi wa malaman makaranta jarrabawar gwaji a Kaduna

A wani labarin daban, gwamnatin jihar Kaduna ta ce za ta sake yi wa malaman makarantun frimare gwajin sanin makamashin aiki a yunkurinta na tabbatar da samar da ilimi mai inganci a makarantun, The Punch ta ruwaito.

Mohammed Mubarak, Mamba na dindindin, Sashin Sanya Ido Kan Ayyuka, Hukumar Kula da Makarantun Frimare na jihar Kaduna ne ya sanar da hakan yayin tattaunawa da manema labarai a Kaduna a ranar Laraba, rahoton Today NG.

Asali: Legit.ng

Online view pixel