Da Dumi-dumi: Ma'aikatan Jiragen Sama Sun Rufe Filin Jirgin Saman Kano
- Harkoki sun tsaya cak a filin jirgin sama na Mallam Aminu Kano a safiyar yau Litinin, 12 ga watan Satumba
- An dai samu sabani tsakanin hukumomin FAAN da NAMA wanda ya kai ga sauke layin wutan dakunan ma’aikatan hukumar da ke kula da sararin samaniyar
- Manyan masu fada aji da abun ya ritsa da su sun shiga tsakani domin ganin harkoki sun dawo a filin jirgin saman
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Kano - Ma’aikatan harkokin jiragen sama sun rufe filin jirgin sama na Aminu Kano saboda sabanin da ya shiga tsakanin hukumar kula da tashoshin jiragen sama ta Najeriya, FAAN, da hukumar kula da sararin samaniyar Najeriya, NAMA.
Jiragen da aka shirya tashinsu daga Kano a safiyar Litinin sun hadu da tangarda yayin da jami’an kula da jiragen sama suka tsayar da ayyukansu cak wanda ya shafi sauka da tashin jirage.
Wani jami’in filin jirgin ya ce an hana jiragen AZMAN da Max Air da suka shirya zuwa Abuja da Lagas tashi, sannan cewa an bukaci fasinjojin da suka shiga jiragen da su sauko domin ma’aikatan jirgin sun dakatar da ayyukansu, Daily Trust ta rahoto.
Takaddama tsakanin hukumomin filin jirgin saman biyu ya fara ne bayan hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta NATCA ta dakatar da zirga-zirgan jirage a ciki da wajen filin jirgin, saboda yanke wutar da aka yi a cibiyoyin NAMA da masaukin ma’aikata.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Solacebase ta rahoto cewa a ranar Juma’a hukumar FAAN ta sauke layin wutan dukkanin masaukin ma’aikatan NAMA saboda rashin biyan kudin wuta.
Majiyoyi sun bayyana cewa manyan mutane da suka yi cirko-cirko a filin jirgin sama, ciki harda wasu yan majalisar dokokin tarayya, mataimakan gwamnoni da sauransu sun fara kokarin yin sulhu don dawo da ayyukan jirage.
Babu shiga, babu fita: Ma’aikata Za Su Rufe Duka Filayen Tashi da Saukar Jirgin Sama
A gefe guda, mun ji cewa ma’aikatan harkokin jiragen sama sun kammala shirin gudanar da zanga-zanga a duka filayen tashi da saukar jirgin sama na kasar nan.
Rahoton Daily Trust na ranar Alhamis, 8 ga watan Satumba 2022, ya bayyana cewa ma’aikatan suna adawa ne ga sabuwar dokar CAA da aka kawo.
Shugaba Muhammadu Buhari ya sa hannu ga dokar harkar jiragen sama watau Civil Aviation Act wanda za ta karawa Ministan harkokin jirage karfi.
Asali: Legit.ng