Bidiyon Yadda Matashi Ya Kera ‘Wheelbarrow’ Mai Amfani da Inji, Ya Ba da Mamaki

Bidiyon Yadda Matashi Ya Kera ‘Wheelbarrow’ Mai Amfani da Inji, Ya Ba da Mamaki

  • Wani fasihi ya girgiza intanet yayin da ya yada wani bidiyo kan yadda ya kirkiri amalanke mai inji
  • An ga karin tayu da tankin man fetur da amalanken ke amfani dashi, hakazalika mutumin ya nuna yadda yake amfani da ita
  • Ana samun matasa hazikai da ke kokarin ganin sauya yadda tsarin abubuwa masu aiki da inji ke tafiya

Duniya na kara ci gaba, a yanzu dai 'yan dako sun kusa daina amfani da karfi wajen tura amalanken daukar kaya saboda wani mutum ya samo musu sauki.

Wani bidiyon da @graphicsengineering ya yada a TikTok ya nuna kirkirar wani bawan Allah, inda aka ga yana gwada wata amalanke mai inji.

Amalanke mai inji ta ba da mamaki a kafar intanet
Bidiyon yadda matashi ya kera 'Wheelbarrow' mai amfani da inji, ya ba da mamaki | Hoto: TikTok/@graphicsengineering.
Asali: UGC

Har yanzu ana kan aikin hada wannan amalanke mai ban mamaki

Lokaci zuwa lokaci, an ce mutumin kan yada bidiyon yadda aikinsa na kirkirar amalanke mai inji ke tafiya daki-daki.

Kara karanta wannan

Mata Da Kudi: Yadda Yan Mata Suka Mato Kan Matashi Dan Tsurut Da Ke Tuka Dankareriyar Jeep Cikin Salo A Bidiyo

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A wani sabon bidiyo, an ga mutumin sakale a kan amalanken da ke tuka kanta da inji ba tare da sa karfi ko turi ba.

Baya ga injin dake makale a jikin amalanken, akwai kuma karin tayu guda biyu da mutum zai iya hawa kai a tsaya.

Hakazalika, akwai kuma ma'ajiyar man fetur da injinta ke amfani dashi.

Kalli bidiyon:

Jama'a sun yi martani

Bayan yada bidiyon, jama'ar intanet sun cika da mamaki, inda suka bayyana martaninsu kamar haka:

@Anything_goes yace:

"Aiki ya yi kyau. Kar ka tsaya, ka bar tarihi kaima dan uwa."

@Obed morrey laurels yace:

"Saura kiris ka kammala dan uwa."

@mkhulisiEC yace:

"Ka yi min kujera, domin ba zan iya wuni a tsaye ba."

Yadda Yajin Aikin ASUU Ya Maida Dalibin Likitanci Mai Siyar da Abinci a Jihar Sokoto

Kara karanta wannan

Ina Mai Rokonka Dan Allah, Ka Kula Da Diyata: Uba Ya Fashe Da Kuka Yayin Da Ya Roki Surukinsa A Bidiyo

A wani labarin, Usman Abubakar-Rimi, wani dalibin ajin karshe a fannin likitanci a Jami’ar Usmanu Danfodiyo Sokoto (UDUS) ya bayyana yadda ya fara sana'ar abinci a kan saboda tsawaitar yajin aikin kungiyar malaman jami’o’i (ASUU).

Idan baku manta ba, ASUU dai ta shiga yajin aikin ne tun ranar 14 ga watan Fabrairun bana, inda ta kora dalibai gidan iyayensu tare da maida su 'yan zaman kashe wando, Daily Trust ta ruwaito.

Abubakar-Rimi ya ce zama bai kama shi ba, domin dole ya nemi abin yi domin kashe lokaci da kuma iya daukar nauyin rayuwa da dai sauran abubuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.