'Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Wani Ɗan Siyasa da Wasu Mutane a Abuja

'Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Wani Ɗan Siyasa da Wasu Mutane a Abuja

  • Miyagun yan bindiga sun yi awon gaba da tsohon Kansila tare da iyalansa mutum Shida a wani sabon harin Abuja
  • Mazauna Anguwar da lamarin ya auku dake wajen birnin Abuja sun ce maharan sun haɗa da wasu mutane 11 ranar Lahadi
  • Basaraken Yaba, Alhaji Abdullahi Adamu, ya tabbatar da lamarin da cewa har fadarsa DPO ya zo domin ya sanar masa

Abuja - Yan bindiga sun sace tsohon Kansilan gundumar Gurdi, yankin ƙaramar hukumar Abaji, Abuja, Muhammad Ibrahim Tanko, da wasu iyalansa Shida.

Daily Trust ta rahoto cewa maharan sun haɗa da wasu mutane 11 sun yi awon gaba da su yayin harin da suka kai ƙauyen Tekpeshe da safiyar Lahadi (jiya).

Harin yan bindiga a Abuja.
'Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Wani Ɗan Siyasa da Wasu Mutane a Abuja Hoto: punchng
Asali: UGC

Wasu rahotanni sun bayyana cewa maharan sun bindige mutum ɗaya har lahira yayin harin. Wani mazaunin yankin yace tsohon Kansilan ya zo ta'aziyya ne lamarin ya rutsa da shi.

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Bude Wuta, Sun Yi Garkuwa da Yayan Ɗan Takarar Gwamna Na PDP a Arewa

Mutumin mai suna Ɗanlami Yakubu yace:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Tsohon Kansilan ya zo ta'aziyyar rasuwar kawunsa, Idris Ibrahim, ranar Asabar kuma yan bindigan sun farmaki ƙauyen ranar Lahadi, suka yi awon gaba da shi da wasu mutum shida a iyalansa, sun kuma ɗauki wasu mutum 11."

Hukumomi sun tabbatar da lamarin

Basaraken Yaba, Alhaji Abdullahi Adamu, ya tabbatar da yin garkuwa da mutanen, inda yace:

"Ina cikin fadata lokacin da DPO na 'yan sanda ya zo domin ya sanar mun da abinda ya faru."

Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan birnin tarayya Abuja, DSP Adeh Josephine, har zuwa yanzun bata turo amsar sakonnin karta kwana da aka aike mata ba kan harin.

Idan baku manta ba a ranar 23 ga watan Afrilu, 2022, wasu yan bindiga suka farmaki ƙauyen Adagba duk a guddumar Gurdi, suka kashe mutum ɗaya suka sace wasu shida.

Kara karanta wannan

Hatsabibin Dan Bindiga Boderi Ya Tsallake Rijiya Da Baya A Yayin Da Sojoji Suka Kashe Mataimakinsa Da Wasu

A wani labarin kuma 'Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Babban Yayan Tsohon Ɗan Takarar Gwamna a Jihar Filato

'Yan bindiga sun kutsa har cikin gida, sun yi awon gaba da babban yayan ɗan takarar PDP da ya nemi tikitin gwamna a jihar Filato.

Mazauna yankin sun tabbatar da faruwar harin ranar Asabar, sun ce maharan sun nemi a tattara musu miliyan N100m na fansa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262