'Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Babban Yayan Tsohon Ɗan Takarar Gwamna a Jihar Filato

'Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Babban Yayan Tsohon Ɗan Takarar Gwamna a Jihar Filato

  • 'Yan bindiga sun kutsa har cikin gida, sun yi awon gaba da babban yayan ɗan takarar PDP da ya nemi tikitin gwamna a jihar Filato
  • Mazauna yankin sun tabbatar da faruwar harin ranar Asabar, sun ce maharan sun nemi a tattara musu miliyan N100m na fansa
  • Jam'iyyar PDP ta nuna rashin jin daɗinta da faruwar lamarin, inda ta yi kira ga gwamnatin Filato ta farka daga bacci

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Plateau - Miyagun 'yan bindiga sun yi garkuwa da Chief Nengak Ropshak, babban yayan tsohon ɗan takarar gwamnan jihar Filato karkashin inuwar PDP, Kefas Ropshak, wanda aka fi sani da Kefiano.

An ce Baban yayan ɗan siyasan ya shiga hannun yan bindiga ne lokacin da suka kai farmaki ƙauyen Rin, ƙaramar hukumar Quaapan a jihar Filato ranar Asabar.

Harin yan bindiga masu garkuwa a Filato.
'Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Babban Yayan Tsohon Ɗan Takarar Gwamna a Jihar Filato Hoto: punchng.com
Asali: Twitter

Mazauna ƙauyen, waɗanda suka tabbatar da faruwar lamarin ga jaridar Punch ranar Lahadi, sun ce masu garkuwan sun tuntuɓi iyalan Ropshak kuma sun nemi fansar miliyan N100m.

Kara karanta wannan

2023: Gwamna Ya Gana da Tsohon Shugaban Kasa, Ya Faɗi Yadda Zasu Kifad Da Atiku a Arewa

PDP Ta Yi Martani

Jam'iyyar PDP reshen jihar Filato, a wata sanarwa da ta fitar, ta nuna kaɗuwa da jin labarin garkuwa da ɗan uwan jigonta.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Sanarwar mai ɗauke da sa hannun Sakataren watsa labarai na PDP, John Akans, wani ɓangarenta yace:

"Jam'iyyar PDP a jihar Filato ta samu labarin garkuwa da Chief Nengak Ropshak a ƙauyen Rin, ƙaramar hukumar Quaapan, cikin takaici da ɓacin rai."
"Chief Nengak, babban yaya ne ga mai girma Chief Kefas Ropshak (Kefiano), wanda ya nemi takarar kujerar gwamna karkashin inuwar PDP. Mun kaɗu da jin labarin sace mutumin."
"An yi garkuwa da shi ne gidansa dake yankin lokacin da yan ta'addan suka kai farmaki, suka buɗe wuta kan mai uwa da wabi daga bisani suka tafi da shi zuwa wani wuri da ba'a sani ba, yanzu suna neman miliyan N100m fansa."

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: 'Yan Bindiga Sun Sake Buɗe Wa Jami'an 'Yan Sanda Wuta, Rayuka Sun Salwanta

Gwamnati ta tashi tsaye - PDP

Bugu da ƙari, jam'iyyar PDP ta yi kira ga gwamnatin jihar Filato ta farka daga baccin da take game da sauke hakkin dake kanta ta hanyar kawo karshe garkuwa da mutane da kashe-kashe ba gaira ba dalili.

"Addu'ar mu na tare da iyalan Chief Kefas Ropshak kan wannan jarabawa mara daɗi da ta afka muku, Allah ya baku ƙarfin cin jarabawan."

Yayin da aka tuntubi kakakin rundunar yan sandan Filato, Alabo Alfred, ba'a same shi ba domin yin tsokaci kan lamarin har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto.

A wani labarin kuma 'Yan Sanda Sun Yi Gumurzu da Yan Bindiga, Sun Ceto Dan Takarar PDP a Jihar Katsina

Gwarazan jami'an yan sanda a jihar Katsina sun kubutar da ɗan takarar kujerar majalisar jiha karkashin inuwar PDP a Kankiya.

Mai magana da yawun yan sanda, SP Gambo Isah, ya tabbatar da nasarar bayan gumurzu da maharan da daren Asabar.

Kara karanta wannan

2023: Daga Karshe, An Warware Saɓanin Dake Tsakanin Atiku da Wike, Ɗan Takarar PDP Ya Faɗi Abinda Ya Rage

Asali: Legit.ng

Online view pixel