Gwamnatin Tarayya Na Daf da Asarar Naira Tiriliyan 7.58 Yayin da Ake Ƙarma-Ƙarma
- Asarar makudan kudi za ta iya hawa kan Najeriya a dalilin rigingimu iri-iri da ake yi da kasar a gaban kotu
- Akwai kamfanonin da suke karar Gwamnatin tarayya, suna neman a biya su diyyar da sun haura N7tr
- Gwamnati tana fama da wadannan matsaloli ne a lokacin da ake kukan babu isasshen kudin shiga a yau
Abuja - Gwamnatin tarayya tana fama da rikici iri-iri a kotu saboda zargin sabawa yarjejeniya. Wannan za su jawowa Najeriya asarar makudan kudi.
Punch a wani dogon rahoto da ta fitar a ranar Litinin, 12 ga watan Satumba 2022, tace gwamnatin tarayya za ta iya rasa kudin da ya zarce Naira tiriliyan 7.
Binciken da aka gudanar ya nuna cewa kamfanonin gida da na ketare dabam-dabam suna shari’a da gwamnatin Najeriya, suna neman kusan N7.58tr.
Kamfanin Sunrise Power Transmission Company of Nigeria Limited ya kai kara a kotun Duniya a Faransa, yana neman gwamnati ta biya shi $400m.
Baya ga haka kamfanin yana shari’a da gwamnatin tarayya a kan wasu $2.354bn da ya kenema a biya saboda sabawa yarjejeniyar aikin wutan Mambilla.
Naira Tiriliyan 6 a tashi daya
A Disamban 2021, wani kamfani mai suna Matreach Logistics Limited ya kai karar NPA da Ministan shari’a, lauyoyinsa su na neman su karbi N6.4tr.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A wannan shari’a mai lamba FCT/CV/408/19 da Onyeka Osigwe da Ekene Arubaleze suka shigar, suna da’awar akwai nauyin hakkokinsu da ke kan gwamnati.
FG v Gwamnonin jihohi
A Agutan bara ne gwamnonin jihohi 36 suka zargi gwamnatin tarayya da karkatar da N1.8tr daga kudin da aka karbo daga hannun barayi da wasu kadarorin N450bn.
Wannan ya jawo aka kai magana gaban Alkali, suna cewa jihohi na da hakki da kudin, amma sai aka jefa su a asusun CRA wanda dokar ka saba ta san da shi ba.
Jaridar tace baya ga wadannan, akwai shari’ar da za ayi da gwamnatin Najeriya a dalilin matakin da aka dauka na jinginar da wasu daga cikin filayen jirgin sama.
An tuntubi Hadimin Ministan shari’a na kasa, Dr. Umar Gwandu game da dukiyar da gwamnati take shirin yin asararsu, amma ya nuna ba zai iya sanin adadin ba.
Babu bata lokaci
Kuna da labari Sanata Kashim Shettima ya bayyana cewa APC mai mulki za ta dankara ‘dan takarar jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar da kasa a zaben 2023.
Sanata Kashim Shettima yace da zarar Bola Tinubu ya zama shugaban kasa, a makon zai rantsar da mutanen da zai yi aiki da su, ba tare da wani bata lokaci ba.
Asali: Legit.ng