NDLEA Tayi Ram da Mai Tsohon Ciki Dauke da Miyagun Kwayoyi
- Jami'an NDLEA sun tabbatar da damke wata mata mai tsohon ciki mai suna Haruna Favour dauke da tulin miyagun kwayoyi
- Kamar yadda kakakin hukumar, Femi Babafemi ya sanar, an kama da methamphetamine tare da nau'ika kala-kala na wiwi
- An kama wasu dillalan kwayoyi a jihohi Gombe, Kogi da kuma Legas kuma duk an yi nasarar dakile safarar kwayoyin
Hukumar yaki da fasa-kwabrin miyagun kwayoyi, NDLEA, ta damke wata mata mai tsohon ciki mai shekaru 25 dauke da kwayoyin methamphetamine a garin Auchi dake jihar Edo.
Kakakin NDLEA, Femi Babafemi, ya sanar da hakan a wata takarda da ya fitar a Abuja ranar Lahadi.
Babafemi yace wacce ake zargin mai suna Haruna Favour, wacce aka kama ranar Juma'a, an kama ta dauke da nau'ikan wiwi da magungunan ruwa masu dauke da codeine.
Yace yunkurin da wasu dillalan kwayoyi suka yi na fitar na 7.805kg na methamphetamine zuwa Amurka da Australia, ya watse bayan jami'an NDLEA sun bankado hakan a Legas.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Babafemi yace an boye miyagun kwayoyin a gefen sutturu, gumakan katako, printer, hannuwan jakunkunan tafiya da garri.
“A wani cigaba na daban, an samo kwayoyin tramadol, D5 da Exol 5 gudan 119,000 daga wasu dillalan miyagun kwayoyi a jihar Gombe.
"Nasiru Abubakar mai shekaru 22 da Umaru Bayero wacce aka fi sani da Hadiza sun shiga hannun jami'an NDLEA bayan jami'an sun kai samame shagunansu dake babbar kasuwar Gombe a ranar Talata, 6 ga watan Satumba."
- Babafemi yace.
Babafemi yace wanda ake zargi mai suna Paul Ali mai shekaru 47 an kama shi a kan babbar hanyar Okene zuwa Abuja a jihar Kogi dauke da kwalabe 1,404 na Codeine masu nauyin 190.94kg.
Yace an kama wasu allurai 2,040 na allurar pentazocine da aka taho da su daga Onitsha zuwa Sokoto.
N50,000 Na Siya Kowanne Daga Cikinsu: Rabaren Sista da Aka Kama da Yara 15
A wani labari na daban, jami'an rundunar 'yan sandan jihar Ribas sun damke wata da ake zargi da safarar yara mai suna Maureen Wechinwu wacce tayi ikirarin ita Rabaren Sista ce kuma siyan yaran tayi.
'Yan sandan dogaro da bayanan sirri sun cafke Maureen a gidanta dake Aluu, karamar hukumar Ikwerre ta jihar Ribas kuma sun ceto yara 15 daga gidan, jaridar Vanguard ta rahoto.
Kwamishinan 'yan sandan jihar, Friday Eboka, ya bayyana cewa an ceto yaran masu shekaru bakwai zuwa tara inda ya kara da cewa za a gurfanar da wacce ake zargi bayan kammala bincike.
Asali: Legit.ng