Da Duminsa: Dakarun JTF Sun Bankado Farmaki a Katsina, Sun Sheke 'Yan Bindiga 9

Da Duminsa: Dakarun JTF Sun Bankado Farmaki a Katsina, Sun Sheke 'Yan Bindiga 9

  • Mambobin CJTF sun dakile mummunan farmakin da wasu gungun 'yan bindiga suka kai garin Batsari na jihar Katsina dauke da muggan makami
  • Zakakuran mambobin CJTF din sun sheke 'yan bindiga tara tare da cafke wasu biyar a yammacin Lahadi yayin da miyagun suka kai hari
  • An gano cewa, 'yan bindigan sun shiga garin a kan babura 10 amma babur 1 kadai ya tsere inda aka kama 9 daga ciki da kuma wadanda ke kai rike da makamai

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Katsina - Wata kungiyar hadin guiwa ta farar hula dake tabbatar da tsaro a karamar hukumar Batsari ta jihar Katsina ta dakile farmakin 'yan ta'adda a garin Batsari.

Kungiyar CJTF din ta yi kokari inda ta halaka 'yan ta'adda tara tare da cafke wasu biyar daga cikin miyagu, jaridar Leadership ta rahoto.

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da 'yan bindiga suka tsare uwa da jaririnta, suna neman fansan miliyoyi

Wata majiya mai karfi ta bayyana cewa, 'yan ta'addan sun kutsa garin wurin karfe 4:30 na yammacin Lahadi a babura kuma rike da miyagun makamai.

Civilian JTF Katsina
Da Duminsa: Dakarun JTF Sun Bankado Farmaki a Katsina, Sun Sheke 'Yan Bindiga 9. Hoto daga leadership.ng
Asali: UGC

Mambobin kungiyar CJTF din sun zage damtse inda suka tunkari 'yan ta'addan tare da hana su farmakin da suka shirya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Majiya tace daga cikin babura 10 da 'yan bindigan suka bayyana a kan su, daya ne kadai ya tsere ya bar garin sakamakon luguden da CJTF din suka musu tare da kama babura tara da suka zo da su.

Kamar yadda yace, 'yan ta'addan sun shiga Batsari cikin kwanakin nan inda suka sace mutane, wannan ne karo na biyu da suka yi yunkuri amma aka dakile su.

Har a halin yanzu, rundunar 'yan sandan jihar Katsina bata fitar da wata takarda kan aukuwar lamarin ba.

Soji Sun Ceto 'Yan Matan Chibok 3, Sun Damke Bukar Abatcha, mai Kaiwa 'Yan Ta'adda Makamai

Kara karanta wannan

Soji Sun Ceto 'Yan Matan Chibok 3, Sun Damke Bukar Abatcha, mai Kaiwa 'Yan Ta'adda Makamai

A wani labari na daban, hedkwatar tsaro a ranar Alhamis ta bayyana cewa dakarun Operation Hadin Kai sun cafke mai kai wa 'yan ta'adda bayanan sirri a yankin Asokoro dake babban birnin tarayya na Abuja.

Hakazalika, sun damke wani 'dan kasar ketare dake samarwa 'yan ta'adda makamai kuma dillalin makamai mai suna Abatcha Bukar tare da wasu 'yan ta'adda 13 a jihar Borno.

Punch ta rahoto cewa, daraktan yada labaran tsaro, Manjo Janar Musa Danmadami, ya bayyana hakan a zantawar da yayi da manema labarai a Abuja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel