An daina daukar mata-maza aikin soja

An daina daukar mata-maza aikin soja

- Shugaba Donald Trump na kasar Amurka ya rattaba hannu akan dokar da tsohon shugaban kasar ta Amurka Barrack Obama ya saka ta hana daukar mata-maza aikin soja a kasar

- Fadar ta sanar da cewar ta dauki wannan matakin ne saboda hakan yana haifar da matsala babba a gidan soja

An daina daukar mata-maza aikin soja
An daina daukar mata-maza aikin soja

Shugaba Donald Trump na kasar Amurka ya rattaba hannu akan dokar da tsohon shugaban kasar ta Amurka Barrack Obama ya saka ta hana daukar mata-maza aikin soja a kasar.

DUBA WANNAN: Mallakar bindiga a kasar Amurka ya zama tamkar ruwan dare

A sanarwar da fadar White House ta fitar ta nuna cewar matakin da shugaban kasar ya dauka ya samu amincewar ministan tsaro na kasar James Mattis. Sannan kuma fadar ta bayyana cewar daga yanzu ta daina daukar duk wadanda keda matsalar al'aura aikin soja.

Fadar ta sanar da cewar ta dauki wannan matakin ne saboda hakan yana haifar da matsala babba a gidan soja, amma fadar ta bayyana cewar akwai yiwuwar a sassauta dokar idan bukatar hakan ta taso.

Bisa dukkan alamu dai shugaba Donald Trump matakin daya dauka yana nuna kalubale ne akan matakin da tsohon shugaban kasar Barrack Obama ya dauka a ranar 1 ga watan Yuli wacce take nuni da bawa mata-maza damar shiga aikin soja a kasar.

Baya da haka shugaba Donald Trump ya kara tabbatar da cewa bayan hana mata-maza shiga aikin na soja, kasar kuma zata daina daukar nauyin wadanda ke canja al'aurar su a asibiti.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng