'Yan Bindiga Sun Rike Jariri da Mahaifiyarsa, Suna Neman Fansan N50m

'Yan Bindiga Sun Rike Jariri da Mahaifiyarsa, Suna Neman Fansan N50m

  • Wata mata dake hannun 'yan bindiga ta haifi jaririnta a mafakar 'yan ta'adda, inji wata majiya daga dangi
  • 'Yan ta'adda na neman kudin fansa har Naira miliyan 50, duk da cewa a baya sun nemi wani adadi mai tsoka
  • Ana yawan samun hare-haren 'yan bindiga da cinikin kudin fansa a yankunan Arewa masu Yammacin Najeriya

Mado, Kaduna - Rahoton da muke samu ya ce, wata mata mai juna biyu da aka sace a Mando ta jihar Kaduna a watan Yulin da ya gabata ta haifi jariri a hannun 'yan bindiga, Daily Trust ta ruwaito.

Matar da aka sacen an ce ta je gaida mahaifiyarta da ke kwance bata da lafiya, an kuma yi awon gaba da ita ne da wasu kannenta mata biyu.

Kara karanta wannan

Yadda Hannu a Karbar Kudin Fansa har N2b da Alaka da Kungiyar Ta'addanci ta sa aka Kama Mamu

Yadda 'yan bindiga suka tsare jariri da mahaifiyarsa
'Yan Bindiga Sun Rike Jariri da Mahaifiyarsa, Suna Neman Fansan N50m | Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

Da yake mai da bahasi game da lamarin, mijin matar, Mohammed Alabi, ya ce:

“Matata ta haihu a mafakar 'yan ta'adda a ranar 2 ga watan Agusta, 2022, kuma tun daga lokacin, uwar da dan ba su samu wata kulawa ba, abin da ma yafi dagula lamari ma shine, mun samu labarin zaluntar dasu ake ana yi musu bulala."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya kuma bayyana cewa, a halin yanzu dai dangi da 'yan uwa na cikin kunci da jimamin halin da baiwar Allahn ke ciki da danta.

Da yake bayyana yadda lamarin ya faru, mahaifin matar, Malam AbdulWahab Yusuf ya ce 'yan bindigan sun kutsa gidan ne dake Mando da misalin karfe 1:05 na rana, inda suka yi barna yadda suka ga dama.

Ya bayyana cewa, 'ya'yansa biyu da aka sace su ke taimakawa mahaifiyarsu da ke kwance bata da lafiya.

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da 'yan ta'adda suka farmaki yankin Kaduna, sun sace mutane, sun kashe wasu

'Yan bindiga na neman kudin fansa

A cewarsa, a baya 'yan bindigan sun nemi a basu kudin fansa da ya kai Naira miliyan 140, amma daga baya suka ce a ba su Naira miliyan 50, BluePrint ta ruwaito.

Kabiru Yusuf, yayan matan da aka sace ya ce, abin da ya dame su a yanzu shi ne, yadda matan suka bayyana cewa 'yan bindigan na cutar dasu ta hanyar yi musu bulala.

Ya yi kira ga gwamnatin tarayya, ta jiha da kungiyoyi masu zaman kansu da su taimaka wajen tabbatar da ceto 'yan uwansa.

'Yan Ta’adda Sun Kashe ’Yan Wasu Uwa 2, Sun Yi Awon Gaba da 13 a Garin Kaduna

A wani labarin, a daren jiya Talata ne wasu gungun ‘yan ta’adda suka farmaki Katun Gida a unguwar Idon dake karamar hukumar Kajuru ta jihar Kaduna, sun kashe wa da kani tare da yin awon gaba da wasu mazauna garin 13.

Kara karanta wannan

Jarabar Mijina ta Ishe ni, Neman Hakkinsa Yake da Azumi ko Ina Al'ada, Matar Aure ga Kotu

Wani malamin addini Katun Gida da ya nemi a sakaya sunansa ya shaidawa jaridar Leadership cewa, lamarin ya faru ne a ranar Laraba 7 ga watan Satumba a Kaduna.

A cewarsa, ‘yan bindigan sun zagaye kauyen ne da misalin karfe 11 na dare, inda suka fara harbe-harbe ba ji ba gani.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.