A Sauya Sunan Aso Rock Ko Sauran Yankunan Arewa Zuwa Sunan Sarauniya Elizabeth, Ohanaeze Ga FG

A Sauya Sunan Aso Rock Ko Sauran Yankunan Arewa Zuwa Sunan Sarauniya Elizabeth, Ohanaeze Ga FG

  • Kungiyar Ohanaeze Ndigbo ta yi martani ga kiran da Adamu Garba yayi na a sakawa jami'ar Nsukka sunan Sarauniyar Ingila Elizabeth
  • Ohanaeze ta ce sunan Sarauniyar Ingila zai fi dacewa da Aso Rock ko sauran yankunan arewa idan har so ake a dunga tunawa da ita
  • Kungiyar Inyamuran ta kuma nemi Garba ya nemi afuwar Ndigbo a kan wannan furuci da yayi, cewa zai iya haddasa rikici a kasar

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Kungiyar Inyamurai ta Ohanaeze Ndigbo, ta bukaci gwamnatin tarayya da ta yi watsi da kiran da aka yi mata na sauyawa jami’ar Najeriya ta NSUKKA suna zuwa na Marigayiya Sarauniyar Ingila.

A cewar kungiyar wannan yunkuri zai fi dacewa ne da fadar shugaban kasa wato Aso Rock a Abuja ko kuma sauran yankunan arewacin kasar, jaridar Punch ta rahoto.

Kara karanta wannan

Jigon APC ya ba Buhari shawarin sauya sunan wata jami'a zuwa sunan sarauniya Elizabeth

Hakan na zuwa ne bayan kungiyar ta jadadda cewa lallai sai tsohon dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Young Progressives Party, Adamu Garba, ya baiwa yan kabilar Igbo hakuri a kan wannan furuci da ya yi.

Sarauniyar Ingila
A Sauya Sunan Aso Rock Ko SauranYankunan Arewa Zuwa Sunan Sarauniya Elizabeth, Ohanaeze Ga FG Hoto: punchng.com
Asali: UGC

A ranar Juma’a ne Garba ya shawarci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya karrama Sarauniya Elizabeth da ta mutu a ranar Laraba, ta hanyar sauya sunan UNN zuwa sunanta.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Sai dai kuma, da yake martani ga lamarin, shugaban Ohanaeze Ndigbo, Chidi Ibeh a wata sanarwa daga babban sakataren kungiyar, Okechukwu Isiguzoro, ya ce irin wannan furucin na iya haddasa rikici a kasar.

Sanarwar ta ce:

“Kungiyar Ohanaeze Ndigbo Worldwide ta gargadi gwamnatin tarayya a kan sauya sunan babbar jami’ar Najeriya, Nsukka zuwa sunan marigayiya sarauniyar Ingila, Sarauniya Elizabeth II.
“Jami’ar na da dadadden tarihi a kudu maso gabashin Najeriya kuma ya kamata tsohon dan takarar shugaban kasar na APC, Adamu Garba ya sani cewa an nadawa cibiyar kiwon lafiya ta tarayya da ke Umuahia, jihar Abia, sunan marigayiya sarauniyar Ingila, kuma ana kiransa da ‘Queen Elizabeth Medical Centre, Umuahia’, amma har yanzu yan Najeriya basu ga wani abu da aka sawa sunan Sarauniya Elizabeth a arewacin Najeriya ba. Yana da kyau arewa ma ta samu wani kaso na abun tunawa da sarauniyar.

Kara karanta wannan

2023: Najeriya Ba Za Ta Zauna Lafiya Ba Idan Mulki Ya Tsaya A Arewa, In Ji PANDEF

“Idan har gwamnatin tarayya da fadar shugaban kasa na son tunawa da marigayiya sarauniya Elizabeth II, sai ta duba rawarganin da sarauniyar ta taka wajen baiwa Najeriya yanci a siyasance da yancin kai a ranar 1 ga watan Oktoban 1960. Kuma wuri da ya fi dacewa don nuna godiya ga Ingila shine Aso Rock.

Jerin Kadarorin da Sarauniya Elizabeth II Ta Bar wa Yarima Charles da Kimarsu

A wani labarin, mun ji cewa Sarauniya Elizabeth II ta rasu a jiya Alhamis 8 ga watan Satumban 2022. Ta shekara 96 kafin Allah ya karbi ranta a gidanta dake Scotland.

Ta bar tarin dukiya mai yawa da aka ce ta kai sama da dala miliyan 500, wanda kuma danta Yarima Charles ne zai gada ya ci gaba da cin duniyarsa da tsinke.

A cewar wani rahoto na Fortunes, mafi yawan kadarorin sarauniyar mallaki ne na Royal Firm, ciki har da dala biliyan 28 na gidan sarautar Burtaniya da Sarki George VI da Yarima Philip suka ambata a matsayin kasuwancin ahali.

Kara karanta wannan

ASUU: An kai makura, gwamnatin Buhari ta yi sabon batu, ta fadi kokarinta a dinke matsalar ASUU

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng