Hotuna Sun Bazu a Intanet Yayin da Sarkin Musulmi Ya Gana da Gwamna Wike

Hotuna Sun Bazu a Intanet Yayin da Sarkin Musulmi Ya Gana da Gwamna Wike

  • Alama na nuna cewa, gwamnan jihar Ribas bai damu da rikicin da jam'iyyarsa ta PDP ke fuskanta ba
  • Gwamna Nyesom Wike ya karbi bakuncin Mai Martaba Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar
  • Wannan ganawa na zuwa ne sa’o’i 24 bayan da jamiyyar PDP ta yi zaman kawo sauyi da dinke barakar cikin gida

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Fatakwal, jihar Ribas - Gwamna Nyesom Ezenwo Wike na Jihar Ribas ya karbi bakuncin Sarkin Musulmi, Mai Martaba Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar a yau Juma'a 9 ga watan Satumba.

Sultan na Sokoto ya ziyarci gidan gwamna Wike da ke Ada George a birnin Fatakwal jim kadan bayan dira a filin jirgin sama na Fatakwal, inji rahoton Daily Trust.

Sarkin Musulmi ya gana da gwamnan jihar Ribas
Gwamna Wike ya karbi bakuncin Sultan na Sokoto, an yada hotunansu a intanet | Hoto: Governor Nyesom Wike - CON
Asali: Facebook

Wike da Sultan sun yi ganawar sirri

Gwamnan na Kudancin Najeriya da kuma shugaba mai fada a ji a Arewacin Najeriya sun yi ganawar sirri.

Kara karanta wannan

Yanzun nan: PDP ta fadi matsayar ta kan ko Ayu zai ci gaba da kasancewa shugabanta

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Sarkin Musulmi ya je Fatakwal ne domin halartar kaddamar da taron kungiyar mata Musulmi ta Najeriya (FOMWAN) karo na 37 na shekara-shekara da suke yi.

Majalisar Zartaswar Jami’iyyar PDP Ta Amince Ayu Ya Ci Gaba da Shugabantar Jam’iyya

Wani rahoton Punch ya ce, majalisar zartaswar jam’iyyar PDP ta kasa ta amince Sanata Iyorchia Ayu ya ci gaba da shugabancin jam'iyyar.

Wannan na zuwa ne bayan majalisar ta NEC ta kada kuri'ar amince da Ayu, wanda hakan ke nufin shugaban jam’iyyar ba zai sauka daga mukaminsa a nan kusa ba.

Ana ci gaba da kai ruwa rana a jam'iyyar PDP game da shugabancin jam'iyyar, tun bayan barkewa rikici tsakanin gwamnan Ribas Wike da dan takarar shugaban kasa na PDP Atiku.

Idan baku manta ba, an samu kiraye-kiraye daga mambobin jam'iyyar PDP kan cewa, ya kamata Ayu ya hakura ya ajiye mukaminsa.

Kara karanta wannan

2023: Jerin Sunayen Yan Takarar Gwamna A PDP Da Suka Ziyarci Wike

Amanata Suka ci kuma Suka Karya Alkawari, Wike ya Fallasa Abinda ya Hadasa da Ayu da Atiku

A wani labarin, gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike ya yi bayanin dalilin da yasa ya fusata da ‘dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar da shugaban jam’iyyar na kasa, Iyorchia Ayu.

Jaridar The Nation ta rahoto cewa, yace yadda suka kasa mutunta yarjejeniya da alkawurran dake tsakaninsu ne ya fusata shi.

Wike yace Ayu ya sha alwashin yin murabus matukar ‘dan takarar shugabancin kasa a jam’iyyar ya fito daga arewa a maimakon kudancin kasar nan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.