Kada Ku Mayar Dani Najeriya, Abba Kyari Zai Iya Kasheni: Hushpuppi Ya Roki Kotun Amurka

Kada Ku Mayar Dani Najeriya, Abba Kyari Zai Iya Kasheni: Hushpuppi Ya Roki Kotun Amurka

  • Ana gab da gama shari'ar Ramon Abbas Hushpuppi da gwamnatin kasar Amurka kan zargin damfara
  • Hushpuppi ya bayyanawa kotu cewa ba zai so ya dawo Najeriya bayan zaman kurkuku ba saboda tsoron Abba Kyari
  • Gwamnatin Najeriya ta ki mika Abba Kyari ga gwamnatin Amurka don binciken alakarsa da Hushpuppi

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Shahrarren dan damfarar yanar gizo, Ramon Abbas, wanda akafi sani da Hushpuppi ya ce dakataccen dan sanda Abba Kyari na iya kasheshi idan gwamnatin Amurka ta mayar da shi Najeriya.

A cewar Peoples Gazette, Hushpuppi ya bayyanawa kotun birnin California cewa tona asirin Abba Kyari da yayi ba karamin hadari ne ga rayuwarsa ba yanzu idan ya koma Najeriya bayan zama a gidan kurkuku a Amurka.

Wannan na kunshe cikin takardar da ya gabatar gaban Alkali Otis Wright inda yake rokon a rage adadin shekarun da ake shirin yanke masa na zaman Kurkuku.

Kara karanta wannan

Kayi Zamanka a Najeriya, Kada Ya Zo Yanzu: Gwamnatin Qatar Ta Aikewa Shugaba Buhari Wasika

Lauyan Hushpuppi, Louis Shapiro, ya gabatar da takardar a madadinsa ranar 5 ga Satumba.

A cewarsa:

"Idan an kammala wannan karar kuma aka saki Mr Abbas, ba zai iya komawa Najeriya ba."

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Abubakar Kyari, dan siyasan Najeriya kuma kwamishanan yan sanda na ka makasa. Abbas na shirin kwashe iyalansa daga Najeriya idan ya fito daga kurkuku saboda barazanar da masoya Kyari ka yiwa iyalansa."
Hushkyari
Kada Ku Mayar Dani Najeriya, Abba Kyari Zai Iya Kasheni: Hushpuppi Ya Roki Kotun Amurka
Asali: UGC

Lauyoyin gwamnatin kasar sun bukaci a yankewa Hushpuppi hukuncin shekaru 11 a gidan kaso kuma ya dawo da $1.7 million da ya sace kuma ya biya tarar $500,000.

Bayan shekaru 11 a tsare, sun bukaci a sakesa amma ya kasance ana bibiyan yadda yake gudanar da rayuwarsa tsawon shekaru uku.

Amma Lauyansa yace Hushpuppi ya zama mutumin kirki tun lokacin da aka kamashi a Dubai.

Saboda haka ya bukaci kotu ta rage zaman gidan kason zuwa watanni 35 zuwa 41.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Shugaban 'yan sanda ya magantu kan yiwuwar yin zabe a shekara mai zuwa

Alkali zai saurari karar ranar 21 ga Satumba sannan ya yanke hukunci.

Babbar Kotun Tarayya Ta Yi Watsi Da Bukatar FG Na Mika Abba Kyari Amurka

A baya mun kawo muku cewa babbar Kotun tarayya da ke zamanta a birnin tarayya Abuja ta yi watsi da bukatar gwamnatin tarayya na tasa keyar dakataccen mataimakin Kwamishinan yan sanda zuwa Amurka.

Alƙalin Kotun, mai shari'a Inyang Ekwo, shi ya yanke hukuncin kan ƙarar da Ministan Shari'a, Abubakar Malami da hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi (NDLEA) suka shigar.

Channels tv ta rahoto cewa, da yake yanke hukunci ranar Litinin, Alƙalin Kotun ya yi watsi da bukatar bisa hujjar cewa ƙarar ta gaza kuma tana da naƙasu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel