Shugaban Buhari Ya Yi Alkawarin Warware Rikicin da Ya Gindaya Tsakanin Mali Cote d’Ivoire

Shugaban Buhari Ya Yi Alkawarin Warware Rikicin da Ya Gindaya Tsakanin Mali Cote d’Ivoire

  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sha alwashin tabbatar wanzuwar zaman lafiya a nahiyar Afrika
  • An samu ballewar rikici tsakanin kasar Mali da Cote D'Ivoire saboda shigar soja ba tare da izini ba
  • Tsohon shugaban kasan Najeriya ya ba Buhari labarin abubuwan dake faruwa, Buhari ya ce dole a dauki mataki

FCT, Abuja - Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Laraba 7 ga watan Satumba a Abuja ya jaddada kudurin Najeriya na wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yammacin Afirka, Daily Nigerian ta ruwaito.

Hadiminsa kan harkokin yada labarai, Femi Adesina ne ya bayyana hakan, inda yace Buhari ya yi magana ne bayan da tsohon shugaban kasa Dr Goodluck Jonathan ya yi masa bayani kan takun sakan dake tsakanin Mali da Cote D’Ivoire.

Kara karanta wannan

Shugaban Kasa Ya Ba Dakaru Wa’adi Domin Ganin Karshen ‘Yan ta’dda da ‘Yan Bindiga

Shugaba Buhari zai dauki mataki kan rikicin Mali da Cote D'Ivoire
Shugaban Buhari ya yi alkawarin warware rikicin da ya gindaya tsakanin Mali Cote D'Ivoire | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Rikici ya barke tsakanin kasashen biyu ne tun bayan da Mali tsare sojojin Cote D’Ivoire 49 saboda shiga kasar ba bisa ka'ida ba.

Rahoto ya bayyana cewa, an saki uku daga cikin sojojin kasancewarsu mata, yayin da wasu 46 ke hannun gwamnatin Mali har yanzu.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Cote D’Ivoire mai makwabtaka da Mali ta yi Allah-wadai da wannan tsare jami'ai nata, inda ta dauki hakan a matsayin yin garkuwa da dakaurunta, tare da bayyana barazanar daukar mataki.

Wanna lamari ya yi kamari, har ya kai tsoma bakin shugabannin ECOWAS kamar yadda jami'in ECOWAS kan halin da ake ciki a Mali, tsohon shugaban kasa Jonathan ya fada.

Femi Adesina ya naqalto cewa, shugaba Buhari ya yi alkawarin kawo wani shiri daga Najeriya da zai gaggauta warware matsalar, rahoton People Gazette.

Mutumin da ya yi yunkurin kashe shugaban kasar Mali ranar sallah ya mutu a magarkama

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: Gwamnatin Buhari Tace Ta Magance Mafi Munin Matsalar Tsaro a Najeriya

A wani labarin, mutumin da ake zargi da kokarin kashe shugaban soja mai karfin iko Assimi Goita, wanda ya kitsa juyin mulki sau biyu a kasa da shekara guda, ya mutu a tsare, in ji gwamnati a ranar Lahadi, 25 ga watan Yulin 2021.

Wanda ake zargin da ba a bayyana ainihinsa ba, an tsare shi bayan yunkurin kisan gillar da ya yi a Babban Masallacin Bamako ranar Talata, Channels Tv ta ruwaito.

"A lokacin bincike...lafiyarsa ta tabarbare" daga nan aka kwantar da shi a asibiti, amma "kash, ya mutu," in ji gwamnati a cikin wata sanarwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.