Matashiyar Budurwar Najeriya Ta Wanke Kafa Har Turai Don Ganawa Da Baturen Da Ta Hadu Da Shi A Yanar Gizo

Matashiyar Budurwar Najeriya Ta Wanke Kafa Har Turai Don Ganawa Da Baturen Da Ta Hadu Da Shi A Yanar Gizo

  • Wata matashiya yar Najeriya ta tafi kasar waje don yin ido hudu da baturen saurayinta ta kuma yada haduwar tasu a soshiyal midiya
  • A cewar budurwar, ta hadu da baturen ne a dandalin kulla soyayya ta kasa da kasa kuma sun shafe tsawon watanni 6 suna soyewa
  • Wani bangare na haduwarsu ta farko ya hasko su kwance kan gado yayin da mutumin mai tsananin kunya ke kokarin gujema kamara

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Wata matashiya yar Najeriya mai suna Kemisola ta hadu da baturen saurayinta da suka shafe tsawon watanni 6 suna soyayya ta yanar gizo.

Budurwar wacce ta cika da farin ciki ta je dandalin TikTok don yada bidiyon haduwarsu ta farko da mutumin.

Budurwa da saurayi
Matashiyar Budurwar Najeriya Ta Wanke Kafa Har Turai Don Ganawa Da Baturen Da Ta Hadu Da Shi A Yanar Gizo Hoto: TikTok/@kemz.o
Asali: UGC

Ta dauki bidiyon yadda ta isa filin jirgin sama na Najeriya tare da wata kawarta sannan ta shiga cikin jirgi.

Budurwar ta kuma baje kolin fasfot dinta a bidiyon. Wani bangare kuma ya nuno ta da wani mutum kwance a kan gado inda yake kokarin guje ma kamara yayin da take daukarsu hoton ‘selfie’.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sai dai babu cikakken bayani game da wacce kasar ta tafi. Da take martani ga jama’a, ta bayyana cewa sun hadu ne a dandalin kulla soyayya.

“Ga mutanen da ke tambayar a wacce dandalin sadarwa muka hadu… Mun hadu ne a dandalin kasa da kasa mai suna internationalcupid."

Kalli bidiyon a kasa:

Jama’a sun yi martani

Blesso ta ce:

“Dan Allah idan yana da wani dan uwa da ke neman budurwa ina nan nagode.”

Zinnie Zinnie ta ce:

“Ya yi kyau! Ki ji dadinki. Allah ne ya baki. Ki fada masa ya yi kama da Phil Collins."

Anita Awa ta ce:

“Wani dandali ne kuke amfani da shi dan Allah ko dai ya banbanta da nawa ne duk da haka na tayaki murna yar’uwa.”

Pinky Juliet ❤️ ta ce:

“Dan Allah a ina kuke ganin saurayi?? Ina taya wata yar’uwa tambaya ne.”

Sai Na Dirje Kafin Na Zabo Mijin Aure Don Ba Zan Taba Auren Talaka Ba, Inji Jarumar Fim

A wani labari na daban, shahararriyar jarumar kasar Ghana, Xandy Kamel, ta bayyana cewa ta yi nadamar auren tsohon mijinta mai suna Kaninja.

Da take zantawa da manema labarai, Kamel ta kuma ce ta yi danasanin auren namijin da bai da kudi da ya amsa sunansa kudi, shafin LIB ya rahoto.

Jarumar ta kuma bayyana cewa ta koyi darasi soasai a aurenta na baya inda ta sha alwashin cewa ba za ta sake auren mutumin da bashi da kudi ba. A cewarta yawancin mazajen da basu da kudi butulu ne kuma mugaye ne sosai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel