Yadda Hannu a Karbar Kudin Fansa har N2b da Alaka da Kungiyar Ta'addanci ta sa aka Kama Mamu
- Majiyoyi daga hukumomin sirri a kasar nan sun ce hannun Tukur Mamu wurin karbar kudin fansa N2b da kai wa 'yan ta'adda na daga dalilin da yasa aka kama shi
- Ba a nan ya tsaya ba kamar yadda majiyar ta bayyana, yana da alaka da wasu manyan kungiyoyin ta'addanci a Sinai dake Misra, Libya da sassan yammacin Afrika
- Majiyar ta jaddada cewa, mamu bashi da gamsasshiyar hanyar samun kudi kamar yadda yake facaka da su, duniya ce ta saka masa ido tun bayan da alakarsa da 'yan ta'adda ta fito fili
Tukur Mamu, mawallafi kuma mazaunin Kaduna an kama shi a Cairo sakamakon zarginsa da ake da hannu wurin karbar kudin fansa tare da kai wa 'yan ta'adda domin sakin wadanda suka sace, Daily Trust ta tattaro daga majiya mai karfi.
Daily Trust ta rahoto cewa, wasu majiyoyin tsaro sun ce baya ga alaka da 'yan ta'addan Najeriya, Mamu ya shiga hannun hukuma ne saboda alakar da yake da ita mai karfin da wata kungiyar ta'addanci a yankin Sinai dake Misra.
Sinai Peninsula yankin arewa maso gabas ne na Misra da ya hada Isra'ila da Gaza ta gabas. Kamar a Najeriya, duk da raguwar yawan hare-haren ta'addanci, 'yan ta'afddan suna nan a yankin kuma sun zama babbar barazana ga jami'an tsaro da sauran Sinai.
Mamu ya musanta aikata wani laifi inda yace yana kan hanyarsa ne ta zuwa kasar Saudi Arabia don yin Umra da iyalansa.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
An zargi hukumomin Najeriya da nuna halin ko in kula ga wadanda aka sace, lamarin da yasa iyalansu suka dinga neman yadda zasu kubutar da su ko ta wanne hali wanda ya hada da bada kudin fansa.
Wannan ne ya kawo shuhurar Mamu bayan ya fito fili tare da bayyana yadda ya karbo wadanda aka sace daga wurin 'yan ta'adda duk da ya musanta karbar kudin fansa daga iyalansu ko kai wa 'yan ta'addan.
Mamu yana cikin jerin wadanda hukumomin tsaron duniya suka sanyawa idanu
Wata majiya daga daya daga cikin hukumomin sirri a Najeriya ta ce kamen Mamu ya biyo bayan harkokinsa na ketare ne ba wai kasar Najeriya kadai ba.
"An kama shi a Misra ne saboda bayanansa dake hannun hukumomin tsaron duniya bayan an sanya masa ido a gida da waje jim kadan bayan farmakin jirgin kasa na Kaduna,
"Ina tabbatar muku cewa Mamu yana da alaka da manyan kungiyoyin ta'addanci a Misra, ballantana a Sinai zuwa Libya har wasu sassan Afrika ta yamma da kuma gabas ta tsakiya."
- Majiyar tace.
"Ya karba kudin fansa N2 biliyan na 'yan ta'adda inda wasu kudin aka biya da dala wanda suka karba daga iyalan wadanda aka sace. Mun dade muna lura da harkokinsa kuma shaidu garemu sosai."
- Majiyar ta kara da cewa.
A yayin da Mamu yace jim kadan bayan saukarsa a Cairo, an so yi masa yadda aka yi wa Nnamdi Kanu, majiyar ta ce:
"Hukumomin Misra basu biyayya ga hukumomin Najeriya. Sun dawo da shi gida ne saboda bayanan da suke da su da kuma dokar duniya."
Wata majiya tace sun dade suna lura da harkokin Mamu na tsawon lokaci kafin a saka masa alamar tamabaya.
"Zai iya sanar da duniya hanyar da yake samun kudi da zai dinga irin rayuwar da yake yi? Da mun so, har gida zamu je a Kaduna mu dauke shi amma saboda abinda yake yi duniya ce ta saka mishi ido, sai muka kyale shi dokokin duniya su hau kansa."
Asali: Legit.ng