Yanzu Nan: DSS ta Magantu Kan Cafke Mamu, Ta Bayyana Dalilinta

Yanzu Nan: DSS ta Magantu Kan Cafke Mamu, Ta Bayyana Dalilinta

  • Hukumar tsaro ta farin kaya, DSS, ta tabbatar da cewa Malam Tukur Mamu yana hannunta bayan an dawo da shi Najeriya daga Cairo, Misra
  • Kamar yadda mai magana da yawun hukumar, Peter Afunanya ya sanar, Mamu yana amsa wasu muhimman tambayoyi kan tsaron wasu sassan kasar nan
  • Afunanya ya sanar da cewa bukatar sojoji da hukumomin sirri na kasar nan ce ta sa aka kama shi kuma za a dauka mataki idan bukatar hakan ta taso

FCT, Abuja - Hukumar tsaro ta farin kaya ta tabbatar da kama Malam Tukur Mamu, tsohon mai sasanci tsakanin 'yan bindiga da 'yan ta'addan da suka yi garkuwa da fasinjojin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna.

Daily Trust ta rahoto yadda aka kama Mamu a filin sauka da tashin jiragen sama na Malam Aminu Kano a ranar Laraba.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Jami'an DSS Sun Cafke Tukur Mamu a Filin Jirgin Kano

Labari da duminsa
Yanzu Nan: DSS ta Magantu Kan Cafke Mamu, Ta Bayyana Dalilinta
Asali: Original

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Mawallafin mazaunin Kaduna na fara kama shi a birnin Cairo dake Misra kuma an tsare shi na sa'o'i 24 kafin a dawo da shi gida Najeriya.

Daily Trust ta lura cewa, yayin da jirgin dake dauke da Mamu da iyalansa ya sauka Kano da karfe 1:55 na rana, an kama shi a filin jirgin da iyalansa.

An kwashe Mamu da iyalansa a motar bas kirar Hiace a yayin da suke saukowa daga jirgin saman da ya dawo da su Najeriya.

A takardar da mai magana da yawun DSS, Peter Afunanya ya fitar, ya tabbatar da kamen Mamu inda yace hukumar tana masa tambayoyi ne a kan wasu lamurran tsaro.

"Hukumar tsaro ta farin kaya tana ta shan tambayoyi kan kamen Tukur Mamu, mai sasanci tsakanin 'yan bindiga da iyalan wadanda aka sace a jirgin kasa.

Kara karanta wannan

Sheikh Gumi Ya Magantu Kan Kamen Hadiminsa, Tukur Mamu, a Kasar Misra

"Muna tabbatar da cewa takwarorinmu na ketare ne suka kama shi a Cairo dake Misra a ranar 6 ga watan Satumban 2022 yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa Saudi Arabia."

- Takardar tace.

"Tuni aka dawo da shi kasar nan a yau 7 ga watan Satumban 2022 kuma hukumar DSS ta karbe shi.
"Wannan bukatar ta biyo bayan bukatar sojojin Najeriya, hukumar tabbatar da doka da bayanan sirri ga takwarorinsu na ketare da su dawo da Mamu kasar nan don amsa muhimman tambayoyi da suka shafi tsaro a wasu sassan kasar nan.
"Ana tabbatar wada jama'a cewa doka zata yi aikinta a duk inda ya dace."

- Takardar ta kara da cewa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng