'Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba da Shugaban Karamar Hukuma, Henry Gotip a Jihar Filato
- Rahotanni daga jihar Filato sun bayyana cewa, wasu tsagerun 'yan bindiga sun yi awon gaba da shugaban karamar hukumar Kanke
- Rundunar 'yan sanda ta tura jami'an tsaro da 'yan banga cikin daji domin tabbatar da an ceto shugaban
- Jihar Filato na daya daga jihohin Arewacin Najeriya dake fama da barnar 'yan bindiga, musamman a shekarar nan
Kanke, jihar Filato - Yanzu muke samun labarin cewa, wasu tsagerun ‘yan bindiga yi awon gaba da shugaban karamar hukumar Kanke ta jihar Filato, Henry Gotip da sanyin safiyar yau Laraba 7 ga watan Satumba.
Rahoto ya ce an sacea Gotip ne a gidansa dake Kwang a karamar hukumar Jos ta Arewa, rahoton jaridar This Day.
Majiya ta ce, an 'yan bindigan sun yi harbe-harbe don tsorata mazauna yankin kafin yin awon gaba da Gotip.
A bangare guda, an ce 'yan bindiga sun farmaki gidan Gotip ne kana suka suka tafi dashi.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Jaridar Punch ta ce ta samo daga tushe cewa, har yanzu dai 'yan bindigan basu tuntubi dangin Gotip ba.
Alfred Alabo, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Filato, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce jami'ai na ci gaba da aiki tukuru don gano inda aka kai shugaban..
Ya ce:
“Kwamishanan ‘yan sanda ya shiga lamarin saboda ya ma tura tawagar jami’an ‘yan sanda zuwa yankin, suna aikin hadin gwiwa da ‘yan banga domin ceto shugaban karamar hukumar."
Kadan daga tarihin Gotip, an ruwaito cewa, shine sakataren kungiyar kananan hukumomin Najeriya a matakin jiha.
Jihar Filato na daya daga cikin jihohin dake fama da barnar 'yan bindiga.
'Yan bindiga sun sace shugaban matasa, sun haɗa da Motoci maƙare da kuɗi a Sakatariya
A wani labarin, 'yan bindiga sun yi awon gaba da wani shugaban matasa a ƙaramar hukumar Ihialia da ke jihar Anambra, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Wata majiya a yankin ta bayyana cewa bayan sace shugaban matasan, maharan sun kai samame Sakatariyar ƙaramar hukuma suka kwashi motoci masu darajar miliyoyin kuɗi da aka tanada son tallafawa mutane.
Shugaban ƙungiyar cigaban matasa ta Okija, Kwamaret Ononuju Maxwell Chigozie, a wata sanarwa ya ce mazauna yankin sun shiga ƙunci sanadiyyar harin.
Asali: Legit.ng