Da Duminsa: Jami'an DSS Sun Cafke Tukur Mamu a Filin Jirgin Kano
- Jami'an hukumar tsaro na farin kaya, DSS, sun cafke Malam Tukur mamu da iyalansa yayin da jirginsu ya sauka a Kano Najeriya
- An tattaro yadda jami'an tsaro da bindigogi suka jira saukar jirgin daga Misra inda motoci suka kwashe Mamu da iyalansa daga saukarsu
- Kamar yadda 'dan uwan Tukur Mamu ya tabbatar, Malamin da iyalansa sun sauka Najeriya amma an kama su, ana kan hanyar kai su Abuja
Kano - Jami’an tsaron farin kaya na DSS, sun kama Malam Tukur Mamu a filin sauka da tashin jiragen sama na Malam Aminu Kano.
Daily Trust ta rahoto yadda ‘yan sandan kasa da kasa suka kama Mamu a birnin Cairo dake Misra kuma aka dawo da shi gida Najeriya.
Tsohon mai sasancin tsakanin ‘yan ta’addan da suka sace fasinjojin jirgin kasan Abuja da iyalansu, yace yana kan hanyarsa ta zuwa Saudi Arabia ne yayin da aka kama shi tare da tsare shi na sa’o’I 24 a Misra.
Daily Trust ta lura cewa, jirgin saman Misra dake dauke da shi da iyalansa ya sauka jihar Kano wurin karfe 1:55 na rana.
Jami’an DSS tuni suka tsaya a hanyar shiga filin jirgin mintuna kafin saukar jirgin saman.
An lura cewa, jami'an tsaro dauke da makamai wadanda ke tare da wasu dake sanye da kayan gida, sune ke tsare da sashin saukar jiragen ketare yayin da ababen hawa uku masu lambar Kano suka tsaya a wurin.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Fasinjoji na fara fitowa daga sashin isowar matafiya, daya daga cikin motocin kirar hilux ta matsa kusa yayin da aka dauka jakunkuna wadanda ake kyautata zaton na Mamu ne da iyalansa, aka zuba su a daya daga cikin motocin.
Daga bisani, an ga yadda motoci biyu suka matsa kusa kuma daya kirar hisce ta matsa kafin daga bisani su bar filin jirgin saman.
An kwashe mamu da iyalansa a motar bas kirar hiace bayan an tsare su a kofar fitowa daga jirgin saman.
'Dan uwan Mamu ya tabbatar da cewa yayaynsa da iyalansa sun iso Najeriya kuma an kama su yayin da ake kan hanyar kai su Abuja.
Wata majiya daga ofishin DSS na Abuja ta tabbatar da cewa an kama Mamu da iyalansa.
Asali: Legit.ng