Yan Ta'addan ISWAP Sun Budewa Yan Ta'addan Boko Haram Wuta
- Jami'an Sojin Najeriya na samun gagarumin nasara kan yan ta'adda masu tada kayar baya a yankin Arewa maso gabas
- Yayinda Suke Gudunma Ruwan Wutan Sojoji, Yan Boko Haram Sun Sha Ruwan Wutan ISWAP
- Yan Ta'addan Kungiyar ISWAP sun kasance yan adawan yan ta'addan Boko Haram, Bal Su suka kashe Abubakar Shekau
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Borno - Wasu yan ta'addan Boko Haram sun yi arangama da yan ta'addan ISWAP yayinda suke kokarin gudun ruwan wutan jami'an Sojojin saman Najeriya a jihar Borno.
Dakarun Sojin Najeriya na cigaba da fitittikan yan ta'addan Boko Haram a yankin Tafkin Chadi.
Wani masanin harkar tsaro a yankin Chadi, Zagazola Makama, ya bayyana cewa ruwan wutan da Sojoji ke yi ya tilastawa yan Boko Haram arcewa daga mabuyansu.
Wata majiya tace:
"Yan ta'addan ISWAP dake Congori da Yuwe sun farmaki yan ta'addan kungiyar Jamā’at Ahl as-Sunnah lid-Da’wah wa’l-Jihād watau Boko Haram."
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Daily Trust ta ruwaito majiyar da cewa yayinda yan ta'addan ISWAP suka hango tawagar yan Boko Haram karkashin jagorancin kwamandoji biyu, sun bude musu wuta.
A cewar majiyar:
"Adadinsu ya wuce 'dari; da yawa cikinsu basu da kaya ko takalmi. Yan kadan cikinsu ke rike da makamai. Babura hudu kacal garesu, da kwamandoji biyu tare da su. Sun jigata kuma wasu ruwa yayi musu duka."
"Yayinda yan ISWAP suka ga akwai mata da yara cikinsu, sai suka barsu suka wuce. Daga baya suka tafi hanyar Bulabulin."
Sojoji Sun Tarwatsa Boko Haram Za Suyi Sallar Gawa, Sun Sake Kashe Na Kashewa
Mayakan Boko Haram da-dama sun bakunci barzahu a wasu danyun hari da dakarun sojojin kasar Najeriya suka kai masu a karshen makon jiya.
A ranar Litinin, 5 ga watan Satumba 2022, an hallaka ‘yan Boko Haram a hare-hare da sojoji suka kai masu.
‘Yan ta’addan sun mutu bayan luguden wuta daga jiragen sojojin sama da kuma rundunar sojojin kasa a wasu artabu da aka yi cikin 'yan kwanakin nan.
Boko Haram sun yi asarar sojoji kimanin 200 da manyan jagororinsu biyar.
Asali: Legit.ng