Yan Bindiga Sun Sake Kashe Fitaccen Malamin Addinin Musulunci A Kudu

Yan Bindiga Sun Sake Kashe Fitaccen Malamin Addinin Musulunci A Kudu

  • Yan bindiga sun farmaki gidan fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Ibrahim Iyiorji, a karamar hukumar Onicha a jihar Ebonyi
  • Maharan da ake zargin yan IPOB ne sun harbi malamin a ranar Lahadi kuma ya mutu ne a ranar Litinin a asibitin koyarwa ta tarayya da ke Abakaliki
  • Kungiyar kare hakkin Musulmi ta MURIC ta yi kira ga gwamnati da ta kamo makasan malamin sannan a gurfanar da su a gaban kuliya

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Ebonyi - Tsagerun yan bindiga da ake zaton yan haramtacciyar kungiyar IPOB ne sun harbe wani shahararren malamin addinin Musulunci a yankin kudu maso gabas, Sheikh Ibrahim Iyiorji.

Maharan sun je har gidan Shehin malamin da ke Isu, karamar hukumar Onicha ta jihar Ebonyi a ranar Lahadi sannan suka harbe shi, jaridar Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Shugaban 'yan sanda ya magantu kan yiwuwar yin zabe a shekara mai zuwa

Malamin ya mutu a daren ranar Litinin a asibitin koyarwa ta tarayya da ke Abakaliki, inda aka kai shi yin jinya.

Yan bindiga
Yan Bindiga Sun Kashe Malamin Musulunci A Ebonyi, MURIC Ta Nemi Gwamnati Da Ta Dauki Mataki Hoto: Channels TV
Asali: UGC

Yayin da take jajantawa al’ummar Musulmin jihar Ebonyi, kungiyar kare hakkin Musulmi ta MURIC ta bukaci hukumomi da su kamo tare da hukunta makasan, rahoton Aminiya.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A cikin wata sanarwa dauke da sa hannun shugabanta na reshen Abuja, Salahudeen Ustaz Yunus, MURIC ta bukaci gwamnati da ta bankado lamuran da ke kewaye da harin.

Sanarwar ta ce:

“Allah ya ba gwamnati ikon yin abun da yakamata wajen gano tushen abun da ke kewaye da harin da miyagun suka kai masa.
“Allah ya saukakawa kowannenmu ta yadda za mu jajirce wajen samun yardarm Allah kafin lokacin mutuwarmu.”

Da aka tuntube shi, kakakin yan sandan jihar Ebonyi, , SP Chris Anyanwu, ya bayyana cewa rundunar bata da masaniya kan wannan lamari.

Kara karanta wannan

Mayakan Boko Haram Sun Kashe Babban Limami Da Wasu Mutum 3 A Jihar Borno

Ya ce:

“Ban ji ba kuma ba a sanar dani cewa abu haka ya faru a karamar hukumar Onicha ba, don haka yadda abun yake kenan.”

Yan Bindiga Sun Toshe Hanyar Kaduna, Sun Kashe Mutum 2 Tare da Sace Matafiya Da Dama

A wani labarin kuma, jaridar Punch ta rahoto cewa yan ta’adda sun toshe hanyar Birnin-Gwari zuwa Funtua, a karamar hukumar Birnin Gwari ta jihar Kaduna.

A yayin harin, maharan sun kashe akalla mutum biyu ciki harda wani direba yayin da suka sace mutane da dama.

Hakan ya kasance ne bayan GOC Division 1 na rundunar sojoji, Kaduna, Manjo Janar Taoreed Lagbaja, ya jagoranci dakaru da suka kai samame kan yan ta’adda a yankunan Birnin Gwari rahoton The Nation.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng