Ambaliyar Ruwa: Ta Karewa Mayakan Boko Haram, Suna Fama Da Karancin Abinci Da Makamai
- Ambaliyar ruwa ta lalata matsugunin mayakan kungiyar ta'addanci da dama inda hakan ya tilasta masu yin kaura da iyalinsu zuwa gefen dajin Sambisa
- Rahotanni sun ce ya Boko Haram na fama da karancin kayan abinci da makamai sanadiyar ambaliyar ruwan da ta daidaita muhallinsu
- Babban kwamandan kungiyar ta'addanci, Goni Farooq, ya mika wuya ga dakarun sojoji a karamar hukumar Bama ta jihar Borno
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Borno - Daily Trust ta rahoto cewa daruruwan mayakan Boko Haram da iyalansu sun kauracewa sansanoninsu yayin da ambaliyar ruwa ta lalata matsuguninsu.
An tattaro cewa wannan barna da ruwan sama yayi ya tilasta masu yin kaura zuwa wasu wurare da ke gefen dajin Sambisa.
A baya mun ji yadda mayaka 70 suka nitse a ruwa sannan rundunar sojojin sama ta yi ruwan bama-bamai a kan wasu wanda yayi sanadiyar mutuwar yan ta'adda fiye da 200 da manyan kwamandoji biyar a karshen makon jiya.
An kuma tattaro cewa batsewar da kogin Yedzaram yayi ya shafi yan ta’adda da dama a sansanonin Sheuri, Kunshe da Gaizuwa a safiyar Lahadi kuma hakan yasa suka gaggauta sauya muhalli.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Aminiya ta kuma rahoto cewa mayakan suna fama da karancin kayayyakin amfani da makamai, kuma sun sauya muhalli zuwa lokacin da za su samu sabbin kaya da dabaru.
Har ila yau, an rahoto cewa Goni Farooq, wani babban kwamandan kungiyar ta’addancin ya mika wuya ga dakarun sojoji a mahadar Banki da ke karamar hukumar Bama ta jihar Borno a ranar Lahadi.
Majiyar tsaro ta bayyana cewa ya fito da wata babur, RPG, bindigar harbin jirgin sama, mujalla 5 da alburusai, na’urar solar, tufafi da sauransu.
Mayakan Boko Haram Sun Kashe Babban Limami Da Wasu Mutum 3 A Jihar Borno
A wani labarin, akalla mutum hudu ne suka mutu ciki harda babban limamin Gima, sannan wasu da dama sun jikkata yayin da mayakan Boko Haram suka farmaki garin Ngulde da ke karamar hukumar Askira-Uba ta jihar Borno.
Mayakan sun kuma sace dabbobi da kayan abinci ba tare da cikas ba, bayan sun cinnawa motoci biyu wuta, kasancewar Ngulde garin manoma ne da ke a wani bangare na dajin Sambisa.
Jaridar Vanguard ta rahoto cewa yan ta’addan da yawansu ya fi 20 dauke da Muggan makamai da bindigogi sun farmaki garin ne tun a ranar Juma’a sannan suka yi barna.
Asali: Legit.ng