2023: Babu Wata Matsala Tsakanin Musulmai da Kiristoci a Najeriya, Babban Malami a Arewa
- Limamin Katolika na jihar Sokoto, Bishop Mathew Kukah, ya bayyana gaskiyar alakar da ke tsakannin kungiyoyin addinai a kasar
- Malamin addinin ya ce ko kadan babu gaba tsakanin Musulmi da Kiristocin Najeriya
- Archibishop na Sokoto ya ce babban matsalar kasar sune shugabanni wadanda ke amfani da addini a matsayin makamin zaluntar mutane
Babban limamin Katolika na Sokoto, Bishop Mathew Kukah, ya ayyana cewa babu watsa matsala tsakanin manyan addinan kasar biyu wato Musulmi da Kirista.
Malamin addinin ya bayyana cewa babban matsalar kasar sune shugabanni marasa kishi wadanda ke amfani da addini wajen juya mutanen Najeriya.
Jaridar Punch ta rahoto cewa Bishop Kukah ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi a shirin gidan talbijin na TVC a safiyar Litinin, 5 ga watan Satumba.
Ya ce:
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
“Babu wata matsala tsakanin Kiristoci da Musulmai. Akwai matsala ne tsakanin shugabanni marasa kishi wadanda basa son yin shugabanci yadda ya kamata, shugabannin addinin kirista marasa kishi wadanda a yanzu suke kallon addini a matsayin makamin zalunci maimakon makamin yanci.
“Wannan shine tushen korafina, saboda wadannan sune bangarorin yin nazari biyu. Na shafe yawancin rayuwata wajen karantar tauhidi da karatun addini da na zamantakewa.”
Malamin addinin ya kuma bayyana cewa kasar nan ta gaza wajen gina shugabanci zai fifita jin dadin al’ummar kasa sama da komai.
Ya bayyana cewa shugabanci na bukatar fifita ra’ayin mutane sama da ra’ayin kashin kai. Ya kuma bayyana cewa akwai bukatar Najeriya ta zama kasa mai mutuntawa da karfafa doka sama da bangarencin addini ko na kabilanci.
Bishop Kukah ya ce ya kamata a bayyana matakin addini a cikin al’umma don gudun haifar da rudani a tsakanin mutanen Najeriya.
Babu Ruwan Coci da Siyasar Jam’iyya, Shugaban CAN Ya Caccaki Wasu Fastoci
A wani labarin, Shugaban kungiyar kiristoci ta Najeriya (CAN), Dr Daniel Okoh, ya shaewarci shugabannin kiristoci a fadin Najeriya da su kauracewa batutuwan da suka shafi siyasa.
Ya kuma shawarci ‘yan Najeriya da su yi karatun ta natsu wajen zaben shugabannin da za su mulke su a nan gaba, rahoton Punch.
Shugaban ya yi wannan kiran ne a garin Onitsha, ranar Lahadi 4 ga watan Satumba a bikin maulidin shekaru 75 na mu'assasin kungiyar Grace of God Mission International, Bishop Paul Nwachukwu.
Asali: Legit.ng