Babban Jam'iyya A Najeriya Ta Dakatar Da Dan Takarar Shugaban Kasarta
- Jam'iyyar African Democratic Congress, ADC, ta sanar da dakatar da dan takarar shugaban kasarta Mista Dumebi Kachikwu
- Hakan na zuwa ne bayan taron da kwamitin NWC na jam'iyyar ta yi bayan wani bidiyo da dan takarar shugaban kasar ya fitar kuma ya bazu a gari
- Jam'iyyar ta zargi Kachikwu da rashin gabatar da tsare-tsaren yadda zai gudanar da kamfen dinsa tun bayan da ya yi nasara a zaben fidda gwani a watan Yuni
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
FCT, Abuja - Jam'iyyar African Democratic Congress, ADC ta dakatar da Dumebi Kachikwu, dan takarar shugaban kasarta, The Cable ta rahoto.
Hakan na zuwa ne awanni bayan da Kachikwu ya goyi bayan kiran da ciyamomin jam'iyyar suka yi na cewa Ralph Nwosu, shugaban jam'iyyar na kasa ya yi murabus bayan shekaru 17 a ofis.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
A cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Asabar, Babajide Ajadi, mataimakin shugaban jam'iyyar na kasa, ya ce kwamitin koli na jam'iyyar wato NEC ce ta dauki matakin a taron da ta yi ranar Juma'a.
Ajabi ya ce tun bayan da Kachikwu ya zama dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar, ya gaza fitar da tsarin yadda zai gudanar da kamfen dinsa da za a fara nan bada dadewa ba.
Ya ce:
"Kwamitin NWC ta nunawa damuwa bisa bidiyon bata suna da Mista Dumebi Kachikwu ya wallafa tare yada wa, da nufin zubar da mutuncin jam'iyyar mu mai nufin kawo zaman lafiya da canji ta African Democratic Congress da shugabanninta na kasa."
"NWC din ta kuma lura tun ranar 9 ga watan Yunin 2022 lokacin da aka zabe shi dan takarar shugaban kasa, ya gaza, ya yi watsi/ya ki nuna wa jam'iyyar tsari mai nagarta ta yadda zai gudanar da kamfen dinsa na shugaban kasa a zaben da ke tafe.
"Abin da ya yi mara kyau, kawo yanzu, yana shafar sauran mambobin mu da ke takarar ofisoshi daban-daban a kasar.
"Kwamitin jam'iyyar, ta yi tir da bidiyon baki dayansa kuma ta bayyana shi a matsayin wani yunkuri na ci da ceto sharri, don haka ta bada shawarar a dakatar da shi daga jam'iyyar nan take yau Juma'a 2 ga watan Satumban 2022."
Ya kara da cewa za a tura wa NEC bayanan domin daukan mataki na gaba.
Jam'iyyar ADC Ta Goyi Bayan Kira Ga Shugaba Buhari Ya Yi Murabus
A wani rahoton, jagororin jam'iyyar African Democratic Party watau ADC sun goyi bayan kiran da ɗan takararsu na shugaban kasa, Mista Dumebi Kachikwu, ya yi na shugaba Buhari ya yi murabus.
Channels tv ta ruwaito cewa ɗan takarar ya yi kura ga shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya yi murabus daga kujerarsa matuƙar ba zai iya haɓaka tattalin arziki da shawo kan matsalar tsaro da suka addabi ƙasar nan ba.
Asali: Legit.ng