Kano: Masu Fadi a Ji Sun Dira Auren Diyar Sarki Aminu Bayero da 'Dan Sarkin Kibiya
- Birnin Kano ya cika dankam da 'yan siyasa da masu mulki a ranar Juma'a yayin da Sarki Aminu Bayero ya aurar da diyarsa ga 'dan Sarkin Kibiya
- Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ne waliyyin amarya inda ya karba sadaki N200,000 tare da daura auren Rukayya da Amir Kibiya
- Gwamna Bello Matawalle, Namadi Sambo, Sarki Nasiru Bayero, minista El-Yakubu, Dambazau, Wamako da sauransu sun halarci daurin auren
Kano - Kwaryar birinin Kano ta cika ta batse a ranar Juma'a yayin da 'dan sarkin Kibiya, Alhaji Umar Usman ya auri diyar Sarkin Kano, Rukayya Aminu Bayero inda manyan mutane suka halarci daurin auren.
Jim kadan bayan addu'o'in, Dr Abdullahi Umar Ganduje wanda ya tsaya matsayin waliyyin amarya, yayi addu'ar Allah ya albarkaci auren tare da basu yara nagari.
An daura auren a fadar Sarkin Kano tare da gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje wanda ya bayar da auren kan sadaki N200,000.
Babban limamin jihar Kano, Farfesa Sani Zahradeen ya yi addu'a ga ma'auratan tare da shawartarsu da su zauna cikin lumana da kwanciyar hankali.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Kamar yadda yace:
"Aure yana da matukar amfani a al'umma. Allah ne ya umarci kowanne Musulmi balagagge wanda ke da aikin yi ko yake da dama da ya aura macen da yake kauna kuma a fara daga biyu, a kafa gida cikin kauna da zaman lafiya."
Manyan bakin da suka halarci daurin auren sun hada da tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Namadi Sambo, karamin ministan ayyuka da gidaje, Umar El-Yakub, gwamnan Zamfara, Bello Matawalle, tsohon gwamnan jihar Sokoto, Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko.
ThisDay ta rahoto cewa, tsohon ministan cikin gida, Abdulrahman Dambazau da Sarkin Bichi, Alhaji Nasir Ado Bayero, suna daga cikin manyan baki.
Hotuna da Bidiyon shagalin Gaɗa da aka yi na bikin Gimbiya Ruƙayya Bayero
A wani labari na daban, bidiyoyi da hotunan shagalin gada ko kuma ranar kauyawa ta auren Fulani Rukayya Bayero sun matukar daukar hankulan jama'a.
Wannan shagalin shine na uku a jerin shagulgulan bikin auren kyakyawar diyar sarkin Kano, Mai Martaba Alhaji Aminu Ado Bayero.
An fara ne da shagalin kamu tun a ranar Lahadi, a ranar Litinin aka biye shi da shagalin Lugude wanda a gargajiyance aka yi shi inda masu kidan kwarya da shantu suka baje kolinsu.
Asali: Legit.ng