Daga Yanzu Dubai Ta Hana Duk Wani Dan Najeriya Mai Kasa Da Shekaru 40 Shiga Kasarta, FG

Daga Yanzu Dubai Ta Hana Duk Wani Dan Najeriya Mai Kasa Da Shekaru 40 Shiga Kasarta, FG

  • Daga Yanzu Gwamnatin kasar Dubai Ta Daina Ba Duk Wani Dan Najeriya Mai Kasa Da Shekaru 40 Bizan zuwa Yawon Shakatawa
  • Daga yanzu duk dan Najeriyan da ke son bizan zuwa shakatawa Dubai ya tafi matarsa da iyali
  • Wadanda aka togaciye a wannan sabuwar doka sune masu iyalai mazauna kasar UAE

Abuja - Gwamnatin Tarayya tayi tsokacin kan halin da wasu yan Najeriya suka shiga yayinda aka taresu a tashar jirgin Dubai, haddadiyar daular Larabawa kuma aka hanasu shiga.

A faifan bidiyon, yan Najeriyan na kukan yadda aka hanasu shiga kasar UAE duk da mallakar biza.

Ma'aikatar harkokin wajen Najeriya ta fitar da jawabi kan wannan lamari.

Dubai
Daga Yanzu Dubai Ta Hana Duk Wani Dan Najeriya Mai Kasa Da Shekaru 40 Shiga Kasarta, FG

Kakakin ma'akatar, Francisca Omayuli, yace laifin yan Najeriyan ne.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

Bidiyoyi: Shigar Kasaita Da Fulani Ruqayya Bayero Tayi A Wajen Dinan Bikinta

A cewarta:

"Ofishin Jakadancin Najeriya dake Dubai tayi fashin baki cewa yan Najeriyan da aka hana shiga sun amshi bizan zasu shiga da iyalansu ne, amma suka isa Dubai su kadai ba tare da iyalansu ba."
"Saboda haka aka korasu su koma Najeriya su nemi Bizan da ya kamata."
"Ya kamata jama'a su sani cewa gwamnatin UAE daga yanzu ta daina baiwa duk dan Najeriya mai kasa da shekaru 40 bizan yawon ganin ido, sai dai wanda zai tafi da iyalinsa."

Ma'aikatar ta yi kira ga duk mai son zuwa Dubai ya fahimci hakan gudun abinda ka iya biyo baya.

Yar Najeriya Da Ke Aiki A Dubai Ta Yi Bidiyon Dakin Da Take Rayuwa Da Gadaje Irin Na Yan Makaranta

Wata matashiyar budurwa yar Najeriya mai amfani da shafin @orobosa2020 a TikTok wacce ke aiki a Dubai tana yawan wallafa bidiyoyin halin da take ciki a bangaren aiki a Dubai.

Kara karanta wannan

Sharruda 5 Da Kasar Dubai Ta Gindayawa Duk Dan Najeriya Mai Son Zuwa Yawon Bude Ido

A daya daga cikin bidiyoyin da ta wallafa a shafinta, matashiyar ta fada kan gadonta mai hawa-hawa irin na daliban makaranta bayan aiki. Sannan akwai wani namiji zaune a sama yana karanta littafi hankalinsa kwance.

A wani bidiyon kuma, an gano ta tana daukar gidan don nunawa mutane irin wajen da take rayuwa a kasar waje.

Asali: Legit.ng

Online view pixel