An Hana Shi Shiga Gidan Casu, Ya Yi Aika-Aika, Ya Yanke Wutar Wurin Gaba Daya

An Hana Shi Shiga Gidan Casu, Ya Yi Aika-Aika, Ya Yanke Wutar Wurin Gaba Daya

  • Wani ta jefa dakin casu cikin duba bayan sanya masa takaicin hana shi shiga a dama dashi a wani taro
  • An ce an hana mutumin shiga farfajiyar dakin taron, lamarin da ya ba shi haushi har ya dauki fansa ta hanyar yanke wuta
  • Faifan bidiyon dake yawa ya nuna lokacin da mutumin ke amfani da karfe wajen datse wutar dake kaiwa ga dakin casun

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

An shiga rudani a wani taron casu da aka hada yayin da wani mutum ya lallaba ta baya ya datse wayar wutar lantarki na dakin taron.

An ce matashin yi wannan aika-aika ne bayan da aka hana shi shiga dakin taron. Maimakon ya koma gida ya ci haushinsa shi kadai, sai ya yanke shawarar daukar fansa.

Yadda wani matashi ya shuka wa masu casu tsiya
Mutumin da aka hana shiga party ya hana kowa zaman lafiya a gidan casu | Hoto: Sestovic and Jasmin Merdan/Getty Images andTikTok/@fleego
Asali: UGC

A wani gajeren faifan bidiyon da aka yada a TikTok, an ga matashin a lokacin da yake datse wayar wutan ta hanyar amfani da karfen yanke wuta.

Kara karanta wannan

Bidiyon Cikin Katafaren Gidan Matashi Dan Shekaru 15, Ya Ce Mawaki Davido Ba Zai Iya Siyan Irinsa Ba

Nan da nan aka ga dakin taron ya shiga rudani saboda yadda matashin ya jefa su a duhu, hakan yasa jama'a suka fara kwada ihu ga kuma sauki ya tsaya.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kalli bidiyon:

Martanin 'yan soshiyal midiya

'Yan soshiyal midiya dai ba su yi shuru ba, sun fadi albarkacin bakinsu.

@youngshaggii yace:

"Amma wannan mutumin ya san kan tsiya."

@kinqbanqs ya ce:

"Har wani taya su yake suna rera waka."

@larrys_collections yace:

"Shikenan ya hana mutane farin ciki."

@davidndavina22 yace:

"Ba ma neman zaman lafiya, kullum tashin hankali muke nema."

@champz148 yace:

"Kuma shi ya fara rera wakar da suke rerawa"

@oplooploo_ yace:

"Ai nan ba wurin ibada bane."

Bidiyon Wani Mutumin da Ya Sanya Takalmi Mai Siffar Kada Ya Girgiza Intanet

Kara karanta wannan

Neman Na Goro: Bidiyon Kyakkyawar Baturiya Tana Tallan Gyada A Titin Lagas Ya Yadu

A wani labarin, caba ado da kwalisa abu ne na ra'ayi, kuma bai cika kawo cece-kuce ba, saboda an ce ra'ayi riga kuma kowa da kalar tasa.

Sai dai, wani ya girgiza ashafukan intanet yayin da yazo da wani sabon salo da ba a saba gani ba, inda ya sanya takalmin da ya jawo cece-kuce.

An ga faifan bidiyon lokacin da yake sanye da takalmi mai siffar kada, kama daga kafar dabbar har zuwa hannaye da gefenta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel