Ku Kama Mazajenku Da Kyau, Maza Tsada Suke A UK: Budurwa Da Ke Turai Ta Shawarci Yan Matan Najeriya
- Wata matashiyar budurwa ta shawarci yan matan Najeriya da ke zuwa UK a kan su rike mazajensu da kyau saboda samun miji na da wuya
- Matashiyar ta bayyana cewa yawancin matan da ke Turai aikinsu suke aure domin samun masoyi na da matukar wahala
- Mutanen da ke zaune a UK sun cike sashin sharhi don gaskata abun da ta fada game da rayuwar Turai
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
UK - Wata matashiya yar Najeriya da ke zama a kasar waje ta yi bidiyo a TikTok, tana mai shawartan yan matan Najeriya a kan kada su zo Birtaniya da tunanin samun miji.
Ta bayyana cewa a UK, aiki shine mazajensu. Budurwar ta shawarci yan matan da ke Najeriya a kan su rike mazajensu da kyau.
Rayuwar aiki kawai ake yi a UK
Mutane sun je sashinta na sharhi don tabbatar da abun da ya fadi game da rayuwar aiki kurum da ake yi a UK.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Kalli bidiyon a kasa:
A daidai lokacin rubuta wannan rahoton, bidiyon ya tattara sharhi sama da 200 da kuma daruruwan “likes”.
Legit.ng ta tattaro wasu daga cikin martanin a kasa:
Thank God ya ce:
“Bamu da lokaci faa. Aikin dare aikin rana. Ya mutum zai yi. Hatta fasto bai ga mabiya ba a ranar Lahadi.”
hotcharles247 ya ce:
“Abun shine saboda yanga da tunkawo ya kashe ku...ku da kuke neman alazawa....lolzzz bari na baki shawara....ki huta ki shirya zuwa bukukuwa...”
Geebaba ya ce:
“Maza na UK kawai dai yawancinku baku san me kuke so bane.”
Tommy-n ta ce:
“Hatta a nan Najeriya babu miji faaa,,,wadanda suka rage yan babi zo gida ne,,,Don haka abun a koina ne.”
Anthony4133 ya ce:
“Kina neman miji ne ki zo garina.”
‘Yar Asalin Jihar Kogi Ta Lashe Gasar Wacce Tafi Kowa Kyawun Fuska A Najeriya A 2022
A wani labari na daban, mun ji cewa budurwa ‘yar shekaru 20, Isa Deborah ta doke sauran takwarorinta wajen lashe gasar wacce tafi kowa kyawun fuska a Najeriya a 2022.
Taron wanda shine karo na tara ya gudana ne a wajen hada sautin kida na Koga da ke yankin Ikeja ta jihar Lagas a ranar 27 ga watan Agusta kuma kamfanin Zanzy Entertainment ne ya dauki nauyinsa.
Deborah dai ta mallaki digiri a bangaren zamantakewa daga babbar jami’ar Abuja kuma ta kasance haifaffiyar karamar hukumar Kabba/Bunu a jihar Kogi.
Asali: Legit.ng